Kwankwaso Ya Ballo Aiki, Kungiyar Yarbawa Ta Yi Masa Raddi kan Sukar Tinubu
- Ƙungigar Afenifere ba ta ji daɗin kalaman da madugun Kwankwasiyya ya yi ba a kan gwamnatin Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- A martanin da ta yi masa, Afenifere ta zarge shi da ƙoƙarin ɓoye gaskiya bayan ya ce Tinubu ya fi fifita wani yanki na ƙasar nan
- Ta nuna cewa kalaman Kwankwaso bai kamata su fito daga gare shi ba, duba da matsayinsa na tsohon gwamna kuma tsohon minista
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere, ƙarƙashin jagorancin Reuben Fasoranti, ta yi kalaman suka kan Rabiu Musa Kwankwaso.
Ƙungiyar Afenifere ta yi watsi da zargin da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kan cewa Shugaba Bola Tinubu na nuna wariya ga yankin Arewa.

Source: Twitter
Sakataren shirye-shirye na ƙasa na ƙungiyar Afenifere, Abagun Omololu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 25 ga watan Fabrairun 2025, cewar rahoton jaridar TheCable.
Kwankwaso ya soki gwamnatin Tinubu
A ranar Alhamis, Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, ya zargi gwamnatin tarayya da mayar da hankali kan wani yanki na ƙasar nan, tana watsi da sauran yankuna.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma yi zargin cewa rashin yin amfani da kuɗade yadda ya dace a matakin ƙasa, jihohi da ƙananan hukumomi ya ƙara tsananta fatara da rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya.
Wane martani Afenifere ta yi wa Kwankwaso?
A martanin da ya yi, Abagun Omololu, ya bayyana iƙirarin Kwankwaso a matsayin “ƙarya mai girma” kuma “magana mai tayar da hankali da gangan", rahoton Premium Times ya tabbatar.
Omololu ya ce abin takaici ne cewa Kwankwaso, wanda ya taɓa zama gwamna da minista, zai yi irin waɗannan maganganun ba tare da la’akari da gaskiya ba.
Ya ce yankin Arewa ya samu gagarumar kulawar gwamnatin tarayya a lokacin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, amma Kwankwaso “ya ƙi bayyana hakan da gangan.”

Kara karanta wannan
"Labarin ƙarya," An ji gaskiyar abin da ya faru kan batun ganawar Tinubu da Kwankwaso
"Babu wani yanki a Najeriya da ya fi Arewa samun damarmakin gwamnatin tarayya a cikin shekaru 10 da suka gabata."
- Abagun Omololu
Omololu ya kawo misalin aikin layin dogo na Kano zuwa Maradi wanda ya zarce zuwa Jamhuriyar Nijar, a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka nuna yadda gwamnatin Buhari ta karkatar da ayyukan ci gaba.
"Shin wannan aikin don haɗin kan ƙasa aka yi shi, ko don sauƙaƙa zirga-zirgar Fulani ƴan uwansa da ke zaune a kan iyaka?"
- Abagun Omololu

Source: Facebook
Ya ce an riga an ba da kwangilar manyan ayyukan tituna a Arewa, ciki har da titunan Kano zuwa Maiduguri, Sokoto-Tambuwal-Jega, da kuma hanyar Abuja-Keffi-Lafia.
Kungiyar da ke rajin kare muradan Yarbawa ta zargi 'dan siyasar da neman tada husuma.
Omololu ya kuma zargi Kwankwaso da ƙarfafa rikicin kabilanci da kuma ƙarfafa ra'ayin ƙarya na cewa ana fifita yankin Kudu fiye da sauran yankuna.
Ministan Tinubu ya dura kan Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan ayyuka, Dave Umahi, ya yi Rabiu Musa Kwankwaso martani mai zafi kan sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC
Ministan ya bayyana cewa zargin da Kwankwaso ya yi na Tinubu yana fifita yankin Kudu fiye da na Arewa babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.
Dave Umahi ya nuna cewa kalaman Kwankwaso suna da haɗari domin za su iya kawo rarrabuwar kawuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
