Gwamnonin 1999 Sun Nemi Tinubu Ya Ajiye Raba Tallafi, Ya Samar da Ayyuka ga Matasa
- Gwamnonin da suka yi mulki a 1999 sun bukaci Bola Tinubu ya fi mayar da hankali kan tsaro da tattalin arziki, ba wai kawai raba tallafi ba
- Tsofaffin gwamnonin sun bukaci kafa masana’antun dogaro da kai a dukkan kananan hukumomi domin rage rashin aikin yi a kasar nan
- Rahoto ya nuna cewa sun ce rabon kudi kamar N5,000 ba zai warware matsalolin da jama’a ke ciki ba, musamman a yankunan karkara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ggwamnonin jihohin Najeriya da suka rike mulki daga shekarar 1999 zuwa 2007, sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali wajen kafa masana’antu.
Sun ce kafa kamfanoni a kananan hukumomi ne zai taimaka wajen samar da ayyukan yi fiye da rabon tallafin N5,000.

Source: Twitter
Vanguard ta rahoto cewa sun fadi haka ne bayan ganawa da suka yi da shugaban kasa a Abuja, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cif Igbinedion ya bayyana cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma noma tare da miƙa shawarwarinsu ga shugaban kasa domin inganta rayuwar talakawa.
Maganar gwamnonin 1999 kan tsaro
Tsofaffin gwamnonin sun bayyana cewa babu wata cigaba da za a iya samu a kasar nan muddin tsaro bai inganta ba.
Sun jaddada cewa dole ne gwamnatin tarayya ta dauki matakai masu karfi don dakile matsalolin tsaro da suka addabi sassan kasar nan.
A cewar Igbinedion:
"Mun shaida wa Shugaban kasa cewa babu ci gaba ko zaman lafiya da za a samu matukar babu tsaro.
Hakan ne ya sa muka bukace shi da ya mayar da hankali wajen tabbatar da tsaro, domin hakan ne tushen komai a kasa."
An nemi samar da aiki maimakon tallafi
Tsofaffin gwamnonin sun ce raba N5,000 ga ‘yan kasa ba shi ne mafita ba, ganin cewa kudin ba zai iya ciyar da mutum ba ko sau daya a rana.
Sun bukaci Tinubu da ya daina wannan salon tallafi maras dorewa, ya koma kan samar da abubuwa more rayuwa da za su kawo canji na hakika.
Punch ta wallafa cewa sun ce:
“Idan mutum ya samu N5,000 da safe, me zai ci da rana? Me zai ci da dare? Wannan ba mafita ba ce. Akwai bukatar mu fuskanci gaskiya cewa wadannan kudi ba sa magance matsalar talauci.”

Source: Twitter
Daya daga cikin manyan shawarwarin da tsoffin gwamnonin suka bayar shi ne gina masana’antun dogaro da kai a matakin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar.
Sun jaddada cewa idan gwamnati ta kirkiro masana’antun da za su dauki jama’a aiki, hakan zai fi amfani a rayuwar talaka fiye da rabon kudi.
An kama wanda ya ce Tinubu ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar DSS ta kama wani matashi a Kano bisa zargin cewa shugaba Bola Tinubu ya rasu a bidiyon bogi.
Rahotanni sun nuna cewa an zargi matashin da hada bidiyo a TikTok da ke nuna shugaban kasar a mummunan yanayi.
Wani lauya, Hamza Nuhu Dantani ya bayyana cewa ba matashin ba ne ya hada bidiyon, ya ce wani ne ya hada shi da fasahar AI.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


