'Yadda Matata Ta Hana Ni Sukar Buhari bayan Ya Mutu': Tsohon Gwamna Ya Magantu

'Yadda Matata Ta Hana Ni Sukar Buhari bayan Ya Mutu': Tsohon Gwamna Ya Magantu

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce matarsa ta hana shi sukar Muhammadu Buhari bayan mutuwarsa a watan Yulin 2025
  • Fayose ya bayyana cewa ba zai iya yabon mamaci idan bai tabuka komai ba, yana mai cewa Najeriya na cikin matsaloli tun zamanin Buhari
  • Ya kare Bola Tinubu, yana cewa yana da saukin kai kuma ya gaji tattalin arziki mai rauni a Najeriya bayan shiga ofis a watan Mayun 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana a karon farko bayan rasuwar Muhammadu Buhari.

Ayo Fayose ya bayyana cewa matarsa ta gargade shi ka da ya furta kalaman suka kan marigayi tsohon shugaban kasa.

Tsohon gwamna ya yi magana bayan rasuwar Buhari
Fayose ya ce matarsa ta hana shi sukar Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari, @GovAyoFayose.
Source: Twitter

Fayose ya yi magana kan mutuwar Buhari

Fayose ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar Buhari, tsohon gwamna ya ji kunya kan kalamansa gare shi da Fulani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fayose na daga cikin gwamnonin da suka yi ta sukar Muhammadu Buhari a lokacin mulkinsu.

Ya ce tabbas matarsa ta taka rawa domin tabbatar da cewa ya guji furta wasu kalamai marasa dadi kan Buhari.

Fayose ya ce:

“Mutane a Najeriya suna yaban mamaci ne kawai. Lokacin da Buhari ya mutu, na so in zage shi, matata ta hana ni yin haka.”

Ayo Fayose ya magantu kan sukar Buhari

Fayose wanda ya saba sukar mulkin Buhari, ya ce har yanzu ra’ayinsa bai canza ba, domin shugaban bai cika burin 'yan kasa ba.

Ya ce:

“Za ka ce Buhari ya yi aiki? Ni ba na daga cikin masu yabon mamaci, Ka da a girmama ni bayan na mutu. Na mutu, na tafi.
“Lokacin da Buhari ke kan mulki, kowa ya san yadda Najeriya take. Kada wani ya zo ya ce Tinubu ba ya kokari."
Fayose ya magantu bayan rasuwar Buhari
Fayose ya fadi yadda matarsa ta hana shi sukar Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari
Source: AFP

Fayose ya kare mulkin Bola Tinubu a Najeriya

Kara karanta wannan

'Ya yi mani albishir zan yi tazarce,' Tinubu ya fadi wanda ya taimaka ya zama shugaban kasa

Yayin da yake kwatanta Buhari da Tinubu, Fayose ya ce shugaban kasa na yanzu yana da saukin kai, kuma shugabancinsa yana da gaskiya.

“Shi (Tinubu) yana da saukin kai. Shin tsohon shugaban yana da saukin kai? Abubuwa da dama suna faruwa a wancan lokaci, ba cikakken mutum ba ne, amma an samu sauyi sosai fiye da baya."

- Cewar Fayose

Ya ce matsalolin Najeriya sun yi kamari matuka, kuma ba za a iya warware su nan take ba ko da da ikon mu’ujiza ne, cewar rahoton Punch.

“Nigeria kasa ce da komai ya lalace; sai sama ta sauko kafin a gyara duka. Wane irin mu’ujiza za a yi cikin shekaru biyu?
“Lamarin ya tsananta matuka, abubuwa sun lalace a wancan lokaci. Tinubu ya gaji tattalin arziki mai matukar rauni."

- Inji tsohon gwamnan Ekiti

Ortom ya magantu kan sukar Buhari

Kun ji cewa tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom ya yi magana game da alakarsa da marigayi Muhammadu Buhari.

Ortom ya ce bai tsani tsohon shugaban kasa Buhari ba kamar yadda ake zargi amma ya soki salon yaki da matsalar tsaro a jiharsa.

A cewar tsohon gwamna Ortom, dole ya fito ya yi magana don kare mutanensa daga hare-haren makiyaya, yana mai cewa ya yi aikinsa ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.