An Daure Wanda Ya Kagi Labarin Rasuwar Bola Tinubu a Mummunan Yanayi
- An zargi wani matashi mai amfani da kafafen sada zumunta ya wallafa bidiyon bogi da ke cewa Shugaba Bola Tinubu ya mutu
- Rahotanni sun bayyana cewa hukumar DSS ta cafke Ghali Isma’il a Kano bayan da ya wallafa bidiyon rasuwar shugaban kasa
- Wani lauya ya bayyana cewa kotun majistare a Abuja ta hana belinsa, ta tura shi gidan gyaran hali har zuwa ranar 19 ga watan Agusta 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, FCT - Wata kotun majistare ta tura wani mai amfani da kafar TikTok, Ghali Isma’il, zuwa gidan gyaran hali na Kuje, bisa zargin yada labaran ƙarya.
Isma’il ya fuskanci tuhume-tuhume biyu da suka shafi wallafa bidiyon ƙarya da nufin tayar da hankalin jama’a da kuma tada ƙiyayya ga gwamnati.

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa

Source: Facebook
Tashar labaru ta NTA ta bayyana cewa an kama matashin ne bisa zargin wallafa bidiyon rasuwar shuagaba Bola Tinubu na bogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar DSS ce ta kama shi bayan ya wallafa bidiyon da ke ɗauke da hoton shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya mutu, inda aka ce bidiyon ya fito daga shafin @bola\_asiwaju a TikTok.
Zargin da ake masa a gaban kotu
An gurfanar da Ghali Isma’il a gaban mai shari’a Ekpeyong Iyang, inda aka karanta masa tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi yada labaran ƙarya da taɗa kiyayya da ɓata suna ga gwamnati.
Lauyan hukumar DSS da na wanda ake tuhuma sun gabatar da hujjojin su a gaban kotu, inda aka nemi beli ga Isma’il, amma kotu ta ki amincewa da hakan.
Mai shari’a Iyang ya umurci a tura Isma’il gidan gyaran hali har zuwa ranar 19 ga watan Agusta domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Lauya ya ce bidiyon mutuwar na bogi ne
A cikin bayani wani lauya, Barista Nuhu Dantani ya yi a Facebook, ya bayyana cewa ba Isma’il ba ne ya kirkiri bidiyon, ya ce wani ne wani ya ƙirƙire shi da fasahar zamani wato AI.
Ya ce:
“Wani bidiyo ya yi da ke nuna shugaban Isra’ila, Natanyahu, yana mutuwa bayan cin abinci mai guba. Amma daga baya aka cire hoton Natanyahu aka maye gurbinsa da na Tinubu.”
Dantani ya kara da cewa, bayan hakan, aka kirkiro asusun TikTok mai suna @bola\_asiwaju aka dora bidiyon, inda hakan ya jawo hankalin DSS da suka kamo Isma’il daga Kano zuwa Abuja.
Barista Dantani ya koka kan yadda jami’an tsaro a Najeriya ke kasa bambance bidiyon da aka yi da AI da wanda ke da sahihanci.

Source: Facebook
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya sanar da labarin kama matashin a wani sako da ya wallafa a X.
An nemi Kwankwaso ya ba Tinubu hakuri
A wani rahoton, kun ji cewa ministan ayyuka na kasa, David Umahi ya yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso martani.
A wani taro da ya halarta a Kano, Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da watsi da Arewa wajen ayyuka.
Sai dai ministan ya bayyana cewa babu gaskiya a zargin da Kwankwaso ya yi tare da cewa ya kamata ya ba Bola Tinubu hakuri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

