Shugaban Ƙasa Guda Ya Baro Ƙasarsa zuwa Daura domin Ta'aziyyar Rasuwar Buhari
- Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, ya kai ziyarar ta’aziyya Daura kan rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
- Barrow ya kai ziyara Daura inda ya gana da iyalan Buhari da kuma Sarkin Daura, yana mai yabon nagartar tsohon shugaban Najeriyan
- Ya ce Buhari ya taimaka wajen tabbatar da dimokuradiyya a Gambiya, yana mai mika sakon ta’aziyya ga 'Yan Najeriya baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Daura, Katsina - Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa garin Daura da ke jihar Katsina.
Barrow ya isa Daura ne a ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025 domin jajantawa iyalan marigayin kan babban rashin da suka yi.

Source: Facebook
Shugaba Barrow ya je Daura ta'aziyyar Buhari
Tsohon marigayin, Bashir Ahmad ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook yayin da Barrow ya ziyarci kabarin Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barrow ya iso filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da misalin ƙarfe 12:35 na rana tare da matarsa, Fatoumata Bah-Barrow.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, da wasu manyan jami’ai ne suka tarbe su a filin jirgin.
Bayan karramawa ta sojoji a filin jirgin, Barrow ya wuce Daura domin ganawa da iyalan Buhari da kuma Sarkin Daura.
Buhari: Wadanda suka tarbi Barrow a Daura
A gidan Buhari, an tarbe shi da ɗansa Yusuf, da ɗan uwansa Alhaji Musa Haro, hakimin Dumurkol, da sauran iyalai.
Barrow ya bayyana rasuwar Buhari a matsayin babban rashi gare shi da kuma nahiyar Afirka gaba ɗaya, yana mai yabon halayensa.
Ya ce Buhari ba kawai shugaba ba ne, amma gwarzo ne da ya tsaya kan gaskiya da hadin kan Afirka.
Ya ce:
“Buhari shugaba ne da ya kware, ya kasance dan’uwa da aboki gare ni, yana da mutunci a fadin Afirka.”

Source: Facebook
Barrow ya yaba da halayen Buhari
Barrow ya ce shi da kansa ya zo domin ya jajanta wa iyalan Muhammadu Buhari saboda irin soyayyar da ke tsakaninsu.
Ya tuna yadda Buhari ya tsaya tsayin daka wajen kare dimokuradiyya a Gambiya a lokacin rikicin siyasa a shekarar 2016.
Ya ce Buhari ya fada masa a kasar Mali cewa “ikon mulki na hannun al’umma,” kalmomin da suka sa shi jajircewa.
Abin da Yusuf Buhari ya fadawa Barrow
Yusuf Buhari ya bayyana godiyarsa ga Barrow, yana mai cewa ziyararsa ta ba su kwarin guiwa sosai.
Yusuf ya ce mahaifinsu ya koya musu gaskiya, da rikon amana, da kada su riki abin da ba nasu ba.
Ya ce kalaman Barrow sun tabbatar da irin mutuncin da mahaifinsu ke da shi har bayan mutuwarsa.
Su wanene ba su je janazar Buhari ba?
Kun ji cewa an gudanar da jana'izar marigayi Muhammadu Buhari a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025 a garin Daura.
Jana'izar ta samu halartar Bola Tinubu da Kashim Shettima da kuma manyan yan siyasa da sarakuna.
Sai dai an yi ta maganganu kan rashin halartar Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje da Sarki Sanusi II da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

