Sarkin Gusau: Rasuwar Basarake Ta Gigita Tinubu, Ya Fadi Alherin da Ya Shuka a Ƙasa
- Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'azziyar rasuwar Sarkin Gusau, Dr Ibrahim Bello wanda ya rasu a safiyar ranar Juma'a bayan fama da jinya
- Tinubu ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi, yana jinjina masa bisa hidimar da ya bayar ga al'umma wanda ba za a manta ba
- Ya mika ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da dangin marigayin, yana rokon Allah ya jikan Sarkin da rahama, ya ba shi kyakkyawan makoma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Rasuwar Sarkin Gusau, Dr Ibrahim Bello ta gigita shugaban kasa, Bola Tinubu inda ya nuna damuwa kan rashin da aka yi.
Shugaba Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sarkin wanda ya cika a safiyar Juma’a 25 ga watan Yulin 2025 a Abuja yana da shekara 71.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa daga mai ba shi shawara kan labarai da dabaru, Bayo Onanuga wanda Punch ta samu.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya fitar da bayanai da mutane ke son sani kan rasuwar Sarkin Gusau
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Dauda ya sanar da rasuwar Sarkin Gudau
Wannan ta'aziyya ta Tinubu na zuwa ne bayan rasuwar marigayin wanda ya shafe tsawon lokaci yana fama da jinya.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal shi ya tabbatar da rasuwar mai martaba Sarkin, Dr. Ibrahim Bello da safiyar yau Juma'a a Gusau.
An tabbatar da cewa Sarkin, wanda ya shafe kimanin shekaru 10 a kan karagar mulki, ya rasu yau Juma'a 25 ga watan Yuli, 2025 yana da shekaru 71 a duniya .
Gwamna Lawal ya yi alhinin wannan babban rashi da jihar Zamfara, Arewa da ma Najeriya gaba ɗaya suka yi, yana mai Addu'ar Allah gafarta masa.

Source: Facebook
Sarkin Gusau: Sakon ta'aziyya daga Shugaba Tinubu
Sanarwar ta ce Tinubu ya bayyana rasuwar a matsayin rashi ba iya Zamfara ba har ma Najeriya gaba daya, cewar Arise News.
Sanarwar ta ce:
“Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin rashi da ya wuce masarautarsa kadai, yana yabawa da hidimar rayuwarsa a matakai da dama.”
Ya kuma mika ta’aziyya ga gwamnatin jihar Zamfara da al’ummar jihar baki daya, da iyalan marigayin, yana rokon rahamar Allah a gare shi.
Sarkin Gusau na 16 ya gaji mahaifinsa wanda ya rasu a ranar 16 ga Maris, 2015 shekaru 10 kenan da suka wuce.
Tsohon jami’in gwamnati ne, inda ya kai matsayin babban sakatare a tsohuwar jihar Sokoto da Zamfara, kuma ya rike sarauta na fiye da shekaru 10.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izar marigayin bayan gabatar da sallar Juma'a a yau.
Farfesa Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Gusau
A baya, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar marigayi Sarkin Gusau yau Juma'a.
Pantami ya bayyana cewa za a yi jana'izar Sarkin da ƙarfe 2:00 na rana a babban masallacin Juma'ar Kanwurin Gusau da ke Zamfara.
Farfesan ya miƙa sakon ta'aziyya iyalan Dr. Ibrahim Bello, ƴan uwa, gwamnatin Zamfara da al'umma tare da addu'ar Allah ya sa shi a Aljannah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
