Bayan Kalaman Kwankwaso, Sarki Sanusi II Ya Yi Jawabi Mai Jan Hankali a Taron Kano

Bayan Kalaman Kwankwaso, Sarki Sanusi II Ya Yi Jawabi Mai Jan Hankali a Taron Kano

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana goyon bayansa ga gwamnatin jihar game da batun gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa
  • Sanusi II ya ce shi da sauran sarakunan Kano za su marawa duk matsayar da Kano ta ɗauka bayan kammala tattara shawarwarin jama'a
  • Kano ta shirya taron shawarwari kan gyaran kundin tsarin mulki wanda Majalisar dokoki ta ƙasa ke yi domin miƙa matsayarta a dunƙule

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi jawabi a wurin taron neman shawarwarin jama'a kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa.

Sanusi II ya ce masarautarsa za ta mara baya ga duk matsayar da gwamnatin Kano da jama’a za su dauka son bada gudunmawa ga gyaran kundin dokokin ƙasa.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Muhammadu Sanusi ya sha alwashin marawa gwamnatin Kano baya Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Sarkin ya bayyana haka a wurin taron da aka shirya don neman shawarwarin jama'a wanda ya gudana ranar Alhamis a fadar gwamnatin Kano, cewar Channels tv.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin da Sanusi II ya yi a taron Kano

Muhammadu Sanusi ya ce masarautun Kano gaba ɗaya za su nazarci shawarwarin da aka gabatar tare da bayar da gudunmawarsu daidai gwargwado.

"Ina yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa matakin gayyatar masu ruwa da tsaki domin bayar da shawarwari kan kudirin gyara kundin tsarin mulki.
"Mu sarakuna, duk abin da gwamnati tare da hadin gwiwar jama’a suka yanke, wanda ya zama matsayar Jihar Kano, za mu mara masa baya dari bisa dari (100%).”
“Za mu duba wannan takarda, mun san muna da wa’adin daga nan zuwa Asabar, idan muna da wata gudunmawa ko gyara, za mu gayyaci kwamitin mu gabatar da shawarwarinmu kafin a gabatar da rahoton ƙarshe.”

Muhammadu Sanusi II ya ba shugabanni shawara

Ya kuma yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki su yi irin hakan, domin zuwa Asabar, za a gama tattara shawarwari wanda shi ne manufar wannan taro.

Kara karanta wannan

"An yi watsi da Arewa," Kwankwaso ya soki Gwamnatin Tinubu, ya faɗi kalamai masu daci

Taron ya bada dama na musayar ra’ayi tsakanin yankuna daban-daban da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a gyaran kundin tsarin mulki domin ya dace da muradun al’ummar Jihar Kano.

Sarkin Kano a taron da gwamnatin Abba ta shirya.
Sanusi II ya ce za su yi nazari kan shawarwarin jama'a a taron da aka gudanar a Kano Hoto: @Husnarh
Source: Twitter

Shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da dama sun halarci wannan taron tattaunawa da nufin inganta tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya ta hanyar sauye-sauyen da suka ƙunshi kowane ɗan ƙasa, rahoton Daily Trust.

Taron, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta, ya samu halaryar manyan masu ruwa da tsaki ciki har da jagoran siyasar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban NNPP na ƙasa, da wasu fitattun 'yan majalisar dokoki.

Sanusi II ya ɗauki zafi kan masu dukan mata

A wani rahoton, kun ji cewa Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a ɗauki tsauraran matakai ga masu aikata cin zarafin matansa ta hannyar dukansu.

Sarki Sanusi II ya nuna matukar damuwarsa kan yadda fyade da kuma yadda mazaje ke dukan matansu ke zama ruwan dare a jihar Kano.

Basaraken ya ƙara da cewa yana da hujja daga Manzon Allah (SAW) cewa duk namijin da zai doki matarsa har ya ji mata rauni ba mutumin kwarai ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262