Bayan Izala da Darika, An Kafa Sabuwar Kungiyar Malaman Addini a Najeriya
- An ƙaddamar da kungiyar Malaman Musulunci Yarabawa a jami’ar Ibadan, don haɗin gwiwa da wayar da kai
- Shugaban kungiyar, Sheikh Khidr Mustapha, ya ce za ta kawo zaman lafiya da inganta koyar da Musulunci
- Manyan malamai, sarakuna da limamai daga jihohin Kudu maso Yamma, Edo da Delta sun halarci taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - An yi muhimmin taron addini a cibiyar Musulunci ta jami’ar Ibadan, jihar Oyo, inda aka ƙaddamar da sabuwar kungiya ta Malaman Musulunci daga yankin Yarabawa.
Kungiya na da nufin ƙarfafa haɗin kai da wayar da kai tsakanin malamai da kungiyoyin Musulunci a shiyyoyi daban-daban.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa taron ya samu halartar manyan malaman addini, kungiyoyi, limamai da shugabanni daga jihohin Kudu maso Yamma guda shida tare da jihohin Edo da Delta.

Kara karanta wannan
Zamfara: An shiga tashin hankali bayan samun gawar malamin Musulunci a mugun yanayi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kafa kungiyar tun watan Agustan 2022, amma yanzu aka fito da ita fili domin gudanar da ayyukanta.
An bayyana cewa kungiyar za ta mayar da hankali kan cigaban dan Adam, tsare akidar Musulunci da yada koyarwar addini ta hanyar alƙur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW).
Manufar kafa kungiyar malaman Musulunci
Shugaban kungiyar, Sheikh Khidr Mustapha, ya bayyana cewa an yi rajistar kungiyar a hukumar CAC, kuma tana da manufar haɗa kan malamai da sake farfaɗo da addini.
Tribune ta wallafa cewa ya ce:
“Wannan kungiya ta bude ƙofa ga dukkan malaman Musulunci da limamai domin haɗa kai da juna don yada addini cikin zaman lafiya da fahimtar juna.”
Ya kuma bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da gudanar da bincike, fitar da fatawowi da bayar da shawarwari kan batutuwan da suka shafi al’umma.
Kungiyar ta nemi haɗin gwiwa da goyon baya
Sheikh Mustapha ya yi kira ga masu hannu da shuni, ‘yan kasuwa, sarakuna da shugabannin siyasa su tallafa wa kungiyar don cimma muradunta.
Ya ce daya daga cikin matsalolin da ke hana cigaban Musulunci shi ne sabani tsakanin malamai da saɓani maras tushe a kafafen sada zumunta.
Shugaban kwamitin shirya taron, Farfesa Ibrahim Otuyo daga jami’ar Al-Ikmah ta Ilorin, ya bayyana cewa an tsara kungiyar cikin tsari mai kyau don gudanar da ayyukanta.
An bukaci sabunta tsarin karatun addini
Limamin masallacin Lekki, Dr Ridwanullahi Jamiu, a cikin wata kasida, ya yi kira da a haɗa sababbin fasahohi da ilimin zamani cikin tsarin karatun addini a jami’o’i.
A cewar shi:
“Akwai bukatar a saka fannoni kamar harkar kudi, likitancin a Musulunci da sauransu domin dalibai su zama masu dogaro da kai,”
Shawarwarin sarakuna da sauran manya
Sarkin Iwo, Oba AbdurRasheed Akanbi, ya bukaci Musulmai su rika shiga harkar siyasa domin kare muradunsu da kare al’ummarsu daga fadawa cikin rashin manufa.

Source: Facebook
Sarkin ya ce:
“Dole ne mu gina kyakkyawan makoma ga ‘ya’yanmu. Siyasa na daya daga cikin hanyoyin cimma hakan.”
Taron ya samu halartar fitattun sarakuna; Oluwo na Iwo da Olowu na Owu Ile, da kuma babban limamin Ibadan, Sheikh Abubakr Agbotomokekere, wanda Mogaji Hassan Onisiniyan ya wakilta.
Haka zalika ya samu halartar manyan limamai daga Ikire da Iwo, Sheikh Muslim Oladiran da Abdulmumeen Muhammad-Thaani.
Rijiyar Lemo ya yi wa dangin Buhari nasiha
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo ya ziyarci iyalan shugaba Muhammadu Buhari.
Malamin ya bukaci iyalan tsohon shugaban kasar da su rika masa addu'a domin samun gafara a wajen Allah.
Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya ce babu wani abu da mamaci ya fi bukata kamar addu'a da iyalan shi za su rika masa bayan ya rasu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

