Gwamnonin da Suka Hana Peter Obi, Wike Ziyartar Jihohinsu a 2025
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya zama gwamna na uku a shekarar 2025 da ya ja kunnen tsohon gwamna kada ya kai ziyara jiharsa saboda dalilan tsaro
- Okpebholo ya yi zargin cewa ziyarar da Peter Obi ya kai jihar a watan Yuni ta haifar da ɓarkewar tashin hankali da kisan mutane biyu a yankin da ya ziyarta
- Peter Obi ya bayar da gudummawar Naira miliyan 15 ga makarantar koyon aikin jinya ta St. Philomena Hospital School of Nursing Sciences yayin ziyararsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Saɓanin da ya ɓarke tsakanin Gwamna Monday Okpebholo na Edo da Peter Obi na jam’iyyar LP ya zama na baya-bayan nan tsakanin tsohon gwamna da wanda ke kan mulki.
Gwamna Okpebholo ya zama gwamnan jam'iyyar APC na biyu da ya buƙaci Peter Obi da ya nemi izinin tsaro kafin ya shigo jiharsu

Kara karanta wannan
Belin dilan ƙwaya: Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamiti game da kwamishinansa a Kano

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce a ranar Juma’a, 18 ga Yulin 2025, gwamnan Edo ya yi zargin cewa ziyarar Peter Obi zuwa makarantar koyon jinya ta St. Philomena ta haddasa sake barkewar rikici da mutuwar mutane uku a yankin.
1. Okpebholo ya gargaɗi Peter Obi
Peter Obi ya kai ziyara makarantar inda ya bayar da gudummawar Naira miliyan 15 domin kammala wasu ayyuka, amma Gwamna Okpebholo ya tambayi inda ya samo kuɗin tun da ya taɓa cewa ba shi da kuɗi.
"Bayan da ya bar wurin, an kashe mutane uku. Saboda haka, Obi bai kamata ya shigo Edo ba ba tare da izinin tsaro ba."
"Ziyararsa ta zo daidai da lokacin da tashin hankali ya sake kunno kai a jihar, kuma ba za mu lamunci hakan ba."
- Gwamna Monday Okpebholo
Magoya bayan Peter Obi da wasu ƴan siyasa, musamman daga kudu maso Gabas, sun soki kalaman Gwamna Okpebholo.
Sai dai, Peter Obi ya dage cewa zai sake zuwa jihar Edo ba tare da ya sanar da gwamnan ba.
Shin Okpebholo ne na farko da ya hana tsohon gwamna ziyartar jiharsa?
Amsar ita ce a’a. Wasu gwamnoni da dama sun taɓa gargaɗin Peter Obi da Nyesom Wike, tsohon gwamnan Rivers kuma ministan babban birnin tarayya Abuja.
2. Gwamna Alia ya hana Peter Obi ziyartar Benue
A tsakiyar watan Afrilu, Peter Obi ya zargi Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue da hana shi ziyartar sansanin ƴan gudun hijira.

Source: Twitter
Sai dai, a cikin wata sanarwa, Kula Tersoo, sakataren yaɗa labarai na gwamnan, ya ja kunnen manyan mutane da kada su shigo jihar ba tare da izinin Gwamna Alia ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ya bayyana cewa ba za a iya tabbatar da tsaron su ba idan gwamnan bai sani ba.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan bai yi tsammanin baƙi a ranar Litinin ba, kuma yana cikin ganawa da manyan jiga-jigai kan batutuwan da ke shafar jihar.
3. Gwamna Diri ya gargaɗi Wike kada ya shigo Bayelsa
Douye Diri, gwamnan jihar Bayelsa kuma jigo a jam'iyyar PDP shi ne gwamna na farko a 2025 da ya ja kunnen tsohon gwamna kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, kada ya shigo jiharsa.
Wasu magoya bayan Wike a Bayelsa sun shirya wani taro da aka shirya ministan zai halarta.
Sai dai Gwamna Diri ya dage cewa Wike ba ɗan Bayelsa bane, kuma bai kamata ya shirya wani taro a cikin jihar mai arziƙin man fetur ba.
Daga baya an yi ƙoƙarin gudanar da taron, amma an tarwatsa mahalartansa da harbe-harbe daga wasu da ba a san ko su waye ba.
Kalli bidiyon maganar Gwamna Diri a nan da tashar Channels TV ta taba wallafawa:
Peter Obi ya tsallake kyautar N120m
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana yadda ya ƙi karɓar kyautar N120m lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.
Peter Obi ya bayyana cewa a lokacin an yi masa kyautar gida wanda darajarsa za ta kai N120m domin bikin murnar cikarsa shekara 50 a duniya.
Sai dai, ya ƙi karɓar kyautar inda ya buƙaci a kai kuɗaɗen a yi amfani da su inda ya dace musamman a fannin ilmi da lafiya.
Asali: Legit.ng

