'Yan Sanda Sun Cafke Budurwar da Ta Kashe Yara 2, An Ceto Jariri

'Yan Sanda Sun Cafke Budurwar da Ta Kashe Yara 2, An Ceto Jariri

  • Jami'an yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata mai suna Esther Gambo da ake zargi da sace wasu kananan yara guda biyu
  • An kama Esther kan sace ‘yan mata biyu ‘yan shekara bakwai a Karamar Hukumar Toro, sannan ta hallaka su a wata gonar masara da gatari
  • Lamarin ya tayar da kura, inda fusatattun matasa suka gudanar da zanga-zanga tare da kona wani coci, har da yunkurin kona caji ofis a Bauchi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wata matashiya ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin yin garkuwa da mutane.

Ana zargin ta da yin garkuwa da ‘yan mata biyu ‘yan shekara bakwai a Karamar Hukumar Toro, sannan ta hallaka su daga bisani.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fatattaki zugar 'yan ta'adda, an aika kusan 95 ga mahaliccinsu

Rundunar yan sandan Najeriya
An kama matar da ta kashe yara a Bauchi Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce an kai rahoton lamarin ne a ranar 22 ga watan Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama budurwa a Bauchi

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa Esther, mazauniyar kauyen Lemoro, ta janyo Khadija Sama’ila da A’isha Dahiru da zummar taimaka musu.

Ta dauke su daga Unguwar Sarkin Yaki da sunan taimako, amma daga bisani ta kashe su a gonar masara da gatarinka.

Ana zargin ta aikata hakan ne domin ta samu damar sace jaririn da wata baiwar Allah mai suna Nafisa Dahiru ta haifa.

An kama mata a Bauchi
Matar ta sace wani jariri bayan kashe yaran a Bauchi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daga baya, dakarun yan sandan sun yi nasarar ceto jaririn da aka sace, yayin da Esther ta shiga hannu kan aika-aikar da ta yi.

Matasa sun yi zanga-zanga a Bauchi

Kisan ya haddasa zanga-zanga da tashin hankali yayin da fusatattun matsa suka kona coci tare da yunkurin kona hedikwatar ‘yan sanda ta Tulu.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun dimauce da aka kai musu hari da dare, an sace shanu

Sai dai jami’an tsaro sun jajirce har an samu dawo da zaman lafiya, inda aka kama mutane 16 da ake zargi da hannu a tarzomar.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bukaci al’umma da su zauna lafiya kuma ya tabbatar da cewa bincike yana ci gaba.

An sace mutane a Bauchi

Wannan lamari na Esther ya zo ne kwanaki kadan bayan an samu labarin garkuwa da mutane da yawansu ya kai akalla 26.

Wasu ’yan bindiga ne suka kai hari a ƙaramar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi, inda suka sace mutane 26 tare da kashe mutum guda.

Wannan lamarin ya faru ne a kauyen Gale da ke cikin gundumar Gwana — yankin da Gwamna Bala Mohammed ya fito.

Matashi ya kashe mahaifinsa a Bauchi

A baya, mun wallafa cewa Wani mummunan lamari ya afku a kauyen Uzum da ke ƙaramar hukumar Giade a jihar Bauchi, inda wani matashi mai suna Limam Muhammad Baba ya kashe mahaifinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Limam da mahaifinsa, Malam Baba Siti, sun samu sabani, wanda daga baya ya kai ga matashin ɗaukar sanda ya daki mahaifinsa sannan ya sara masa kai.

Bayan faruwar lamarin, an kai rahoto ga ofishin ’yan sanda na Giade da misalin ƙarfe 10.30 na dare, kuma rundunar ta tura jami’anta zuwa wurin da abin ya faru, inda aka cafke Limami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng