Sheikh Pantami Ya Fitar da Bayanai da Mutane ke Son Sani kan Rasuwar Sarkin Gusau

Sheikh Pantami Ya Fitar da Bayanai da Mutane ke Son Sani kan Rasuwar Sarkin Gusau

  • Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da cewa za a yi jana'izar Marigayi Sarkin Katsinan Gusau yau Juma'a
  • Pantami ya bayyana cewa za a yi jana'izar Sarkin da ƙarfe 2:00 na rana a babban masallacin Juma'ar Kanwurin Gusau da ke Zamfara
  • Malamin ya miƙa sakon ta'aziyya iyalan Dr. Ibrahim Bello, ƴan uwa, gwamnatin Zamfara da al'umma tare da addu'ar Allah Ya sa shi a Aljannah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gusau, jihar Zamfara - An fara miƙa sakon ta'aziyya da alhini bayan rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Mai Martaba Dr. Ibrahim Bello.

Sarkin na Gusau ya rasu ne da safiyar yau Juma'a, 25 ga watan Yuli, 2025 bayan fama da doguwar jinya, yana da shekaru 71 a duniya.

Farfesa Isa Ali Pantami.
Sheikh Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

A wani sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Isa Ali Pantami ya fitar da ƙarin bayani kan jana'izar marigayi Sarkin.

Kara karanta wannan

Sanadiyyar rasuwar Sarkin Gusau da gwagwarmayar da ya yi a rayuwar shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Pantami ya yi alhinin rasuwar Sarkin Katsinan Gusau tare da addu'ar Allah Ya masa rahama kuma Ya karɓi baƙuncinsa.

Pantami ya fitar da bayanin janazar Sarkin Gusau

Da yake ƙarin bayani kan shirye-shiryen jana'iza da lokaci, Pantami ya tabbatar da cewa za a yi wa marigayin sutura a yau Juma'a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Sheikh Pantami ya sanar da cewa za a yi wa Sarkin jana'iza da misalin ƙarfe 2:00 na rana, ma'ana bayan sallar Juma'a a babban Masallacin Juma'a na Kanwurin Gusau.

Ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan sarki, gwamnatin jihar Zamfara da ɗaukacin al'umma bisa wannan babban rashi na uba da aka yi a Arewacin Najeriya.

Sheikh Pantami ya yi ta'aziyyar Sarkin Gusau

A sanarwar da Pantami ya fitar, ya ce:

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un. Muna mika taaziyyar rasuwar Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, (Sarkin Gusau), Dr Ibrahim Bello wanda Allah Ya dauki rayuwarsa a yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta jijjiga Arewa, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau ya rasu

"Za'a masa Sallar Janaza da karfe 2:00 da rana a yau Juma'a, a Babban Masallacin Jumu'ah na Kanwurin Gusau in Allah Ya yarda.
"Muna ta'aziyya zuwa ga iyalansa da yan'uwansa da talakawansa, da Gwamnatin Jihar Zamfara, tare da adduar Allah Ya sa Aljannah ce makomarsa tare da iyayenmu da malamanmu da zurriyyarmu da yan'uwanmu."
Pantami ya yi jimamin rasuwar Sarkin Gusau.
Pantami ya ce za a yi jana'izar Sarkin Gusau da ƙarfe 2:00 na rana Hoto: Professor Isa Pantami
Source: Facebook

Marigayi Dr. Ibrahim Bello ya shafe tsawon shekara 10 a sarautar Sarkin Gusau bayan naɗinsa a 2015, kamar yadda DCL Hausa ta rahoto.

Abubuwan sani game da Sarkin Gusau

A wani labarin, Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan sani game da marigayi Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello.

Sarkin Gusau da ke jihar Zamfara ya hau karagar mulki a 2015 kuma ya yi aiki da hukumomin lafiya da ilimi kafin samun sarauta.

Kafin ya zama sarki, marigayin ya shahara a aikin gwamnati, inda ya fara aiki da asibitin Gusau a 1977 bayan kammala karatu a makarantar jinya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262