Rikici Ya Kaure a tsakanin Jagororin Majalisa, Akpabio zai Iya Samun Matsala
- Hatsaniya ta kaure a zauren majalisa tsakanin shugabanta, Sanata Godswill Akpabio da shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele
- Wannan ya biyo zargin da ake yi wa Akpabio na tafiyar da al'amuran majalisa na tare da tuntuɓar sauran jagororinta ba
- Sanata Bamidele da Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume sun bayyana rashin jin daɗin yadda ake tafiyar da al'amuran majalisa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Wasu sababbin rikice-rikice na shirin kunno kai a cikin shugabancin majalisar dattawan Najeriya.
Shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya samo Shugaban majalisar, Godswill Akpabio kan tsarin tafiyar da shugabanci.

Asali: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wannan takaddama ta faru ne a zauren majalisa a ranar Laraba, kuma wasu majiyoyi na cewa rikicin ya samo asali ne tun a shekarar 2023.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai saɓani a majalisar dattawa
Sahara Reporters ta ruwaito cewa ana hasashen ƴar tsama da ta shiga tsakanin Akpabio da Bamidele kan zaben shugaban majalisa ya ci gaba da jawo matsala har yanzu.
Sai dai an samu masu kokarin musanta rahotannin da ke nuna cewa akwai sabani a shugabancin majalisar.
Rahoton ya ce tarzoma ta fara ne bayan Akpabio ya sanar cewa majalisar za ta tafi hutun shekara, amma da alamun cewa ba a yi wannan zance a tsakanin shigabannin ba.
Ana ganin wannan batu ne da ya kamata Akpabio ya gana da wasu daga cikin manyan jagororin majalisa a kai kafin a zo batun sanar wa a zauren.
Sanatoci sun buga muhawara kan umarnin Akpabio
A zaman majalisa, an buga muhawara kan ko an yi zaman kwanaki 181 kafin sanar da hutun, kamar yadda ya ke a dokar kasa.
Wani Sanata da ya nemi a sakaye sunansa ya ce:
“An samu cece-kuce kan ko mun kammala zama na kwanaki 181 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Wannan kuwa abu ne da ya kamata a fara tattauna wa a tsakanin shugabanni kafin a fito da shi a zauren majalisa.”
Sanatan ya kara da cewa Akpabio ya ce za a yi taron NEC na jam’iyyar APC a ranar Alhamis, don haka suka ga dacewar kammala zama a ranar Laraba.
Amma Sanata Bamidele ya dage cewa ba su kai kwanakin da ake bukata kafin ƴan majalisa sun tafi huhu ba.
An yi mamakin musayar yawu a majalisa
Duk da cewa Bamidele na da hujjar doka a maganarsa, rahotanni sun nuna cewa ya ba da mamaki ganin yadda ya fito karara yana kalubalantar shugaban majalisar.
A cewar wani Sanata:
“Ba daidai bane a yi haka a zauren majalisa. Amma gaskiya Akpabio ya nuna kwarewa da sanin ya kamata ta hanyar shawo kansa cikin ladabi."

Asali: Facebook
Majiyar ta kara da cewa:
“Tuni ake cewa Akpabio baya hada kai da sauran shugabanni. Daga mataimakin shugaban majalisa har zuwa shugaban masu rinjaye, da yawa daga cikinsu ba sa sane da abubuwan da ke faruwa."
Bayan jawabin Bamidele, Sanata Ali Ndume daga Borno ta Kudu shi ma ya bayyana rashin jin dadinsa a kan yadda Akpabio ke tafi da majalisa.
Jam'iyyar APC ta kara ƙarfi a majalisa
A baya, kun ji cewa kam’iyya mai mulki ta APC na dab da cimma rinjaye na kaso biyu bisa uku a Majalisar Dattawa da ake bukata wajen yanke hukunci kan ƙudurori.
Wannan na nufin idan haka ta tabbata, gwamnatin tarayya ba ta buƙatar wasu Sanatoci daga jam'iyyun adawa kafin tabbatar da wani ƙuduri ya zama doka.
Hakan ya samu bayan wasu sanatoci daga jam’iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC, kuma yanzu ana buƙatar Sanatoci biyu kawai don ta kai matakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng