Gwamnatin Abba Ta Dura kan Bangaren Lafiya, Za a Gyara Asibitoci sama da 200 a Faɗin Kano

Gwamnatin Abba Ta Dura kan Bangaren Lafiya, Za a Gyara Asibitoci sama da 200 a Faɗin Kano

  • Gwamnatin Kano ta ayyana shirin fara gyara cibiyoyin lafiya 203 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar
  • Sanarwar da Ibrahim Adam, hadimin gwamnan Abba Kabir Yusuf ya fitar ta ce tuni aka fara aikin a ƙaramar hukumar Bichi
  • Ibrahim ya kara da cewa matakin na ƙara nuni ga kudurin gwamnatin Kano wajen fara aikin nan da gaggawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A wani mataki na inganta rayuwar al'ummar jihar Kano, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ɗauko wasu manyan ayyuka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na ya amince da gyaran cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 203 da ke cikin kananan hukumomi 44 na jihar.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano za ta gyara asibitoci Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A saƙon da Ibrahim Adam, mai na gwamna shawara kan harkokin yada labarai ya wallafa a shafin Facebook, tuni aka fitar da jerin asibitocin da za a tashi komaɗarsu.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, an hangi Kwankwaso a wurin taro tare da Gwamna Abba da Sarkin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba: Gwamantin Kano za ta gyara asibitoci

Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka fara aiki a wasu cibiyoyin, musamman a karamar hukumar Bichi, tare da wasu yankuna.

Ta ce cewa kowace karamar hukuma a Kano za ta amfana da cibiyar lafiya mai inganci da kayan aiki na zamani.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf
Za a gyara asibitoci 200 a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Sanarwar ta kuma ce wannan aikin gyara na zuwan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da haɓaka wasu cibiyoyi 18 na lafiya matakin farko zuwa matakin biyu.

Wasu asibitocin Kano da za a gyara

Sanarwar ta kuma jero wasu daga cikin asibitocin da za su samu gyara a dukkanin ƙananan hukumomi 44.

Sun haɗa da;

1. Karamar hukumar Bebeji

  • Asibitin Anadariya
  • Asibitin Gargai
  • Asibitin Durmawa Health Clinic
  • Asibitin Tariwa
  • Asibitin Wak
  • Asibitin Rahama

2. Karamar hukumar Bichi

  • Asibitin Kwamrawa
  • Asibitin Chiromawa

Asibitin Damargu 3. Karamar hukumar Dala

  • Asibitin yara da karbar haihuwa na Gwammaja
  • Asibitin Adakawa
  • Asibitin karɓar haihuwa da yara na Dala
  • Asibitin sha ka tafi na Dandinshe firamare

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yi zarra, Abba ya ƙara samun lambar gwarzon gwamnoni a Najeriya

4. Karamar hukumar Kumbotso

  • Asibitin Ahmad Ado Bayero
  • Asibitin Challawa
  • Asibitin Panshekara
  • Asibitin Riga Fada

5. Karamar hukumar Sumaila

  • Asibitin Gala
  • Asibitin Rimi
  • Wurin shan karbar magani na Garfa
  • Asibitin Massu

6. Karamar hukumar Tarauni

  • Asibitin Yar Akwa
  • Asibitin Daurawa
  • Asibitin Gyadi-Gyadi Kudu
  • Asibitin Hausawa
  • Asibitin Jaoji

7. Ƙaramar hukumar Doguwa

  • Karamin asibitin Burji
  • Asibitin Danyar Shere
  • Asibitin Rirwai
  • Asibitin Tagwaye Health Clinic

Waɗannan na daga cikin asibitoci 203 da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya gano suna da buƙatar a yi masu gyara don amfanin al'umma.

Gwamnan Kano Abba ya yi zarra

A baya, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo a matsayin gwarzon gwamnoni na shekarar 2025.

Jaridar Blueprint da ta shirya karramawar ta ce ta ɗauki matakin ne saboda gagarumin aikinsa a bangaren raya ilimi da ci gaban dan Adam a jihar.

Masu shirya taron sun bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki matakai masu kyau na farfado da makarantun gwamnati da suka lalace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng