Dara Ta ci Gida: Kotu Ta Umarci Ƴan Sanda Su Biya Masu Zanga Zanga Diyyar N10m
- Wata kotu a Lagos ta umarci babban Sufetan yan sanda ya biya N10m ga masu zanga-zangar EndSARS bisa take hakkinsu na 'yan kasa
- Alkalin kotu ya ce ’yan sanda sun ci zarafin masu zanga-zanga duk da ’yancinsu na taro da walwala bisa kundin tsarin mulki
- Masu kara sun hada da kungiyoyi da dama kamar ERC, TIB da CDHR da wasu mutane 23 da aka ce an ci zarafinsu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Wata kotu a ranar Alhamis 24 ga watan Yulin 2025 ta yi zama kan shari'ar da ake karar rundunar yan sanda.
Mai Shari'a, Musa Kakaki na Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ya ci tarar rundunar yan sanda saboda cin zarafin masu zanga-zanga.

Source: Twitter
Matakin da kotu da dauka kan yan sanda
Leadership ta ce alkalin ya umurci Sufeto Janar na ’Yan sanda da ya biya N10m a matsayin diyyar cin zarafinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan zanga-zangar wasu masu fafutukar rajin sauyi da suka halarci bikin cika shekara hudu na zanga-zangar EndSARS.
Yayin da yake yanke hukunci a karar da masu fafutukar suka shigar, alkalin ya ce masu karar suna da ’yancin taro da walwala kamar yadda sashe na 40 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.
Gargadin kotu ga 'yan sanda kan bin doka
Kotun ta kuma bayyana cewa, ko da yake ’yan sanda na da ikon aiwatar da doka, dole su yi hakan bisa ka’idar dimokuradiyya da dokar kasa.
Kotun ta kara da cewa an ci zarafin masu karar, wadanda suka halarci zanga-zangar a ranar 20 ga Oktoba, 2024, ba bisa ka’ida ba kuma an tauye musu ’yancin su.

Source: Facebook
Zanga-zanga: Wadanda ke karar rundunar yan sanda
Masu karar sun hada da Uadiale Kingsley, Ilesanmi Kehinde, Osopale Adeseye, Olamilekan Sanusi, Hassan Taiwo Soweto, cewar The Guardian.
Sai kuma Akin Okunowon, Ugochukwu Prince, Osugba Blessing, Kayode Agbaje, Michael Adedeji, Jennifer Rita Obiora, Orunsola Oluremi, Seyi Akinde da Aisha Omolara.
Sauran sun hada da Isaac Obasi, Funmilayo Jolade Ajayi, Thomas Abiodun Olamide, Ogbu Obinna Ferdinald, Aghedo Kehinde Stephen, Duronike Olawale, Gideon Adeyemi, da Afeez Suleiman.
Har ila yau, daga cikin kungiyoyi masu karar akwai 'Campaign for the Defence of Human Rights (CDHR)', 'Education Rights Campaign (ERC)' da 'Take It Back Movement (TIB)'.
An gudanar da zanga-zangar tsofaffin 'yan sanda
A wani labarin, tsofaffin ‘yan sanda na kasa sun isa Abuja domin gudanar da babbar zanga-zanga saboda tsarin kudin fansho wanda ake zargin babu tsari a cikinsa.
'Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, da wasu masu fafutuka sun gudanar da zanga-zanga a birnin tarayya wanda aka shirya musamman saboda tsofaffin yan sanda.
Rundunar ‘yan sanda ta zargi wasu da amfani da batun jin dadin jami’an da suka yi ritaya don cimma wata manufa ta su ta karan kansu da ta ganin ya saba doka.
Asali: Legit.ng

