Nentawe: Alkawuran da Shugaban APC Ya Daukar Wa Jam'iyya bayan Tafiyar Ganduje
- Sabon shugaban APC na ƙasa, Farfesa Yilwatda Nentawe, ya ce zai haɗa kai da kowa domin faɗaɗa jam’iyyar a fadin Najeriya
- Nentawe ya bayyana hakan ne a jawabin karɓar mukami yayin taron NEC na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis
- Hope Uzodimma ne ya gabatar da kudirin zabar Nentawe daga Arewa ta Tsakiya, wanda Kakakin Majalisa, Tajuddeen Abbas ya mara wa baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Sabon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Yilwatda Nentawe ya karbi shugabancin jam'iyyar.
Nentawe ya ce zai haɗa kai da kowa cikin jam’iyyar a faɗin ƙasa domin dawo da martabarta a idon yan Najeriya.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya ce a yau ne aka tabbatar da Nentawe a matsayin sabon shugaban APC a taron NEC a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Murabus din Ganduje ya ba Nentawe kofa
Nentawe ya karbi shugabancin jam'iyyar bayan murabus din tsohon gwamNan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Murabus din Ganduje ya ba mutane mamaki duba da yadda ya ajiye aikin a lokacin da ba a taba tsammani ba.
Sai dai wasu rahotanni sun yi zargin cewa Ganduje ya ajiye aikin ne bayan matsin lamba daga fadar shugaban kasa sabanin zargin cewa kula da lafiyarsa ne dalilin murabus dinsa.
Alkawuran da Nentawe ya daukar wa APC
Yayin da yake jawabi bayan karbar rantsuwa a Abuja, Nentawe ya bayyana irin salon shugabanci da zai yi.
Ya ce:
“Ina alkawari ba tare da jinkiri ba cewa zan yi aiki da kowa a cikin jam’iyyar… Zan faɗaɗa jam’iyyar tare da ku.
Taron ya gudana ne a cibiyar taro ta fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis 24 ga watan Yulin 2025.

Source: Twitter
Yadda Nentawe ya zama shugaban jam'iyyar APC
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda ke jagorantar Ƙungiyar Gwamnonin APC, ne ya gabatar da kudurin karkatar da shugabancin jam’iyyar zuwa Arewa ta Tsakiya.
Daga nan sai Uzodinma ya gabatar da Nentawe a matsayin ɗan takarar shugabancin jam’iyyar bayan murabus din Abdullahi Ganduje.
Kakakin Majalisar Wakilai ta tarayya, Hon. Tajudeen Abbas, shi ne ya mara wa kudurin baya yayin taron da aka gudanar.
Nentawe, ɗan asalin jihar Plateau, daga yankin Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Har ila yau, kafin zama shugaban APC, shi ne ya ke rike da mukamin ministan jin kai da walwalar jama'a, cewar Vanguard.
Nentawe: Abubuwan sani game da sabon shugaban APC
Mun ba ku labarin cewa a yau Alhamis 24 ga watan Yulin 2025 aka rantsar da sabon shugaban jam'iyyar APC ta kasa a birnin Abuja.
An nada Farfesa Yilwatda Nentawe ne daga jihar Plateau a Arewa ta Tsakiyar Najeriya bayan murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan rahoton ya yi duba kan wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Farfesan wanda ya rike mukamin ministan jin kai da walwala kafin karbar shugabancin APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

