Bayan Taron Daidaita Farashin Fetur, Shettima Ya Yi Magana kan Tallafin Mai
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce cire tallafin mai na daga cikin sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya yi don kishin kasa
- Ya bayyana cewa wasu ‘yan ba ni-na-iya na a harkar mai sun yi kokarin hana cire tallafin, amma shugaban kasa ya tsaya kai-da-fatarsa
- Shettima ya yi magana ne kwana guda bayan kammala taron Afrika ta Yamma kan daidaita farashin man fetur a babban birnin tarayya, Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa matakan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke dauka suna da amfani ga daukacin ‘yan Najeriya.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar kasuwanci da masana’antu ta kasa, wato NACCIMA, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa ya ce gwamnati ta tanadi yanayin da ya dace domin inganta harkokin kasuwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cire tallafin man fetur da gyaran tsarin musayar kudi a matsayin wasu daga cikin sauye-sauyen da suka fi muhimmanci a wannar gwamnatin.
Maganar Kashim Shettim kan tallafin mai
Shettima ya ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna jarumta wajen daukar matakin cire tallafin mai, duk da irin adawar masu ruwa da tsaki a harkar man fetur suka nuna.
A cewarsa:
"Wannan gwamnatin taku ce, domin Shugaban kasa na sauraron 'yan kasuwa. Ya taso a cikin kasuwanci, ya san yadda ake tafiyar da kasuwanci, kuma shi ne tsohon mai kula da kudi a kamfanin Mobil.”
Ya ce duk da cewar wasu da ke rike da manyan rassa a harkar mai sun yi yunkurin dakile cire tallafin, Shugaban kasa bai yarda ba.
“Yan-ba-ni-na-iya a harkar mai sun yi yunkuri su hana, amma ya tsaya da kafarsa saboda kishin kasa,”
- Inji Shettima.
Magana kan sauye sauyen gwamnati
Mataimakin Shugaban kasar ya ce gwamnatinsu ta dauki matakai da dama domin farfado da tattalin arzikin kasa da kuma samar da cigaba mai dorewa.
Rahoton 21st Century Chronicle ya nuna cewa ya ce:
“Na yarda cewa Najeriya ta shirya wajen gudanar da harkokin kasuwanci na gaskiya.
Shettima ya kara da cewa sauye-sauyen haraji da tsarin canjin kudi na daga cikin matakan da ke taimakawa wajen dawo da amincewar ‘yan kasuwa.

Source: Getty Images
Shugaban NACCIMA ya bayyana burinsu
Tun da farko a jawabinsa, shugaban NACCIMA, Jani Ibrahim, ya bayyana cewa ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kungiyar wata daya da ya gabata a Ilorin.
Ya ce kungiyar su za ta ci gaba da ba da hadin kai ga gwamnati wajen samar da mafita ga matsalolin tattalin arziki da suka addabi ‘yan kasuwa da masana’antun cikin gida.
Ibrahim ya bayyana jin dadinsa kan yadda gwamnati ke bude kofar shawarwari ga ‘yan kasuwa domin gina kasa mai karfi da ci gaba.
An yi taro kan farashin mai a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta jagoranci taron kasashen Afrika ta Yamma kan daidaita farashin mai.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa 'yan Afrika ba za su zuba ido suna kallo ana sanya wa albarkatunsu farashi a duniya ba.
Legit Hausa ta rahoto cewa an gudanar da taron ne a ranakun 22 zuwa 23 ga Yuli 2025 a wani dakin taro a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng


