Ana Fargabar Kusan Mutum 50 Sun Mutu a Hadarin Jirgin Rasha da Ya Kama da Wuta
- Jirgin sama ya yi hadari a dajin Amur, inda rahotanni suka ce ana farbagar babu wanda ya tsira daga cikin mutum 49 da ke cikin jirgin yayin tashin sa
- Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya kama da wuta yayin kokarin sauka a yanayi mai hadari, kuma ba a ga wanda ya tsira ba daga binciken sama da aka gudanar
- Jami'an agaji sun bayyana cewa jirgin mallakin kamfanin Angara ne, kuma ya bace ne kafin ya isa yankin Tynda, a nan aka hango ya fadi cikin daji
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Russia - Wani mummunan hadarin jirgin sama ya afku a gabashin kasar Rasha inda wani jirgi dauke da mutum 49 ya fadi ba tare da an sami wanda ya tsira ba.
An bayyana cewa jirgin yana kan hanyarsa daga Blagoveshchensk zuwa garin Tynda lokacin da ya yi hadarin.

Source: Getty Images
Rahoton Sky News ya nuna cewa gwamnan yankin Amur, Vasily Orlov, ya tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Vasily Orlov ya ce jami’an ceton gaggawa dauke da kayan aiki na musamman sun kai agaji wurin da jirgin ya fadi.
Wani bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta ya nuna jirgin ya fadi cikin daji mai cike da bishiyoyi, sai aka ga wuta na tashi daga bangaren jirgin kafin ya kai kasa.
Me ya haddasa hadarin jirgi a Rasha?
Rahoton hukumar agajin gaggawa na yankin ya bayyana cewa jirgin ya fadi ne a wani waje mai nisan kilomita 15 a Kudu da garin Tynda.
Ana zargin cewa wani kuskure ne yayin kokarin saukar gaggawa ya haddasa hadarin jirgin saman.
Jami’an ceto sun bayyana cewa jirgin ya nemi sauka har sau biyu kafin a daina samun bayanai game da shi.
Jami’an bincike daga ofishin mai kula da zirga-zirgar sufuri sun bayyana cewa za a cigaba da bincike har sai an gano ainihin musabbabin hadarin.
Mutane nawa ne a cikin jirgin?
Jirgin da ya yi hadarin nau'in Antonov An-24 ne, wanda aka kera tun shekarar 1976 kuma jirgin yana karkashin wani kamfani mai zaman kansa da ke cikin yankin Siberia.
Wani jirgi mai saukar ungulu kirar Mi-8 mallakin hukumar sufurin jiragen saman Rasha ya hango karafunan jirgin suna ci da wuta.
Rahoton Al-Jazeera ya bayyana cewa adadin mutanen da ke cikin jirgin ya kai 49 ko kuma kasa da hakan, amma dai babu wanda ya tsira daga ciki har yanzu.

Source: Getty Images
Wata jami’ar hukumar agaji, Yuliya Petina ta bayyana cewa:
“A yayin binciken farko, an hango jirgin na ci da wuta. Jami’an agaji na kokarin isa wurin hadarin.”
Hukumomin Rasha sun bayyana cewa an riga an fara bincike kan hadarin, domin gano ko akwai wani sakaci ko gazawa da ta kai ga hakan.
An samu gawar tsohon ministan Rasha
A wani rahoton, kun ji cewa an samu gawar tsohon ministan sufurin Rasha a wani yanayi mai tayar da hankali.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama a kasar Rasha sun nuna damuwa kan samun gawar tsohon ministan.
Lamarin ya dauki hankali ne lura da cewa ba a dade da korar shi daga aiki ba aka samu gawar shi, abin da ya jefa zarge zarge.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


