'Zai Zama Mana Jangwangwan': APC Ta Ƙi Aminta da Shigowar Gwamnan PDP

'Zai Zama Mana Jangwangwan': APC Ta Ƙi Aminta da Shigowar Gwamnan PDP

  • Jam’iyyar APC ta jihar Osun ta yi magana da ake ta jita-jita cewa Gwamna Ademola Adeleke zai dawo cikinta
  • APC ta ƙi karɓar Gwamna Adeleke saboda a cewarta bai da tasiri kuma zai iya lalata sunan jam’iyyar mai-ci
  • Shugaban APC, Tajudeen Lawal ya ce Adeleke na neman mafaka a APC saboda fargabar faduwa a zaɓen 2026

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Jam’iyyar APC reshen jihar Osun ta yi fatali da maganar cewa Gwamna Ademola Adeleke zai dawo cikinta.

APC ta ce ba ta aminta da Gwamna Ademola Adeleke da zuwansa jam’iyyar ba saboda zai zama nauyi gare ta.

APC ta soki gwamnan PDP kan shirin dawowa cikinta
APC ta ƙo aminta ta shigowar gwamnan PDP. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

APC ta kwancewa gwamna zani a kasuwa

A cikin wata sanarwa ranar Laraba, shugaban APC na Osun, Tajudeen Lawal, ya ce Adeleke na neman mafakar siyasa ne, cewar TbeCable.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan PDP, shugabanninta sun ba maraɗa kunya, sun goyi bayan Tinubu a fili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lawal ya ce hakan wata dabara ce domin samun mafaka a APC kafin zaɓen gwamna na shekarar 2026.

Lawal ya ce an gano cewa gwamnan tamkar wata cuta ce wanda sauya shekar sa zai jawo matsala ga martabar APC.

Zarge-zargen da APC ke yiwa jam'iyyar PDP

Ya kuma zargi shugabannin PDP da yaudarar jama’a da cewa Adeleke ne jam’iyyar APC ta ƙi karɓa.

Ya ce:

“Jama’ar Osun sun sani cewa gwamnan ya nemi mafaka a APC saboda tsoron faduwa a 2026.
“PDP ta zama kamar gida mai cike da masifa, ‘yan siyasa masu hankali sun gudu. Abin da ya rage ragowar ‘yan siyasa ne marasa tasiri.”
"Jam'iyyar PDP ta rasa mutunci tun bayan 2023 kuma yanzu “mallakar dangin Adeleke ce ta zama jam’iyyar.”
“Mutane masu basira da suna, waɗanda ba za su iya jure yaudara da rashawa da mulkin danniya na Adeleke ba, kullum na sauya sheƙa zuwa jam’iyyarmu.

Kara karanta wannan

APC ta ji ba dadi bayan jin labarin Tinubu ba zai samu karbuwa ba a 2027

- Cewar Lawal

APC ta tozarta gwamnan PDP a Osun
APC ta cire kunya bayan rade-radin gwamnan PDP zai dawo cikinta. Hoto: Gov. Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

APC ta fadi dalilin kin Gwamna Adekeke

Lawal ya kuma ambaci “kisan magoya bayan APC” da ba a warware ba a zaɓen baya a matsayin dalilin da ya sa aka ƙi Adeleke.

Shugaban APC na Osun ya kuma zargi wasu jiga-jigan PDP da cin hanci, yana cewa EFCC da ICPC na binciken su.

Lawal ya ce yaudara ce ga Adeleke ya soki gwamnatin Tinubu a Osun, amma ya yi kamar aboki ne a Abuja, cewar Vanguard.

A cewarsa, jama’ar Osun sun gaji da mulkin Ademola Adeleke kuma sun yi murna da yadda sauya shekarsa zuwa APC ta ci tura.

Lawal ya ce Adeleke da PDP su daina kuka, su shirya su fuskanci hukuncin masu zaɓe a shekarar 2026.

Gwamnan PDP zai marawa Tinubu baya a 2027

Kun ji cewa shugabannin PDP a jihar Osun sun bayyana matsayarsu game da zaben 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

PDP na shirin taron NEC don duba tsarin karɓa karɓa, ta yi wa Tinubu saukale

Shugabannin jam'iyyar da Gwamna Ademola Adeleke sun tabbatar da cewa za su goyi bayan Bola Tinubu a 2027.

Hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamna Adeleke zai bar PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel