Zamfara: Mutane Sun Gaji da Hare Haren 'Yan Bindiga, Sun Nuna Fushinsu ga Gwamnati
- Mazauna wasu ƙauyukan jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana kan matsalar rashin tsaro
- Sun koka kan yadda ƴan bindiga suke cin karensu babu babbaka ta hanyar kashe mutane tare da sace su a kowace rana
- Mutanen dai sun isa har gidan gwamnatin Zamfara domin nuna fushinsu kan yadda ƴan bindiga suka addabe su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ɗaruruwan mazauna ƙauyuka daban-daban na ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Laraba.
Mutanen sun fito zanga-zangar ne don nuna rashin jin daɗinsu kan ƙara tsanantar rashin tsaro, inda suka zargi ƴan bindiga da kashe mutane kusan 100 a kowace rana a ƙauyukan da abin ya shafa.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa masu zanga-zangar sun fito ne a ƙafa, a kan babura da motoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane sun fito zanga-zanga a Zamfara
Masu zanga-zangar sun haddasa tsaiko wajen zirga-zirga a Gusau, babban birnin jihar, na tsawon fiye da sa’o’i biyu, inda suka toshe manyan hanyoyi kafin su nufi gidan gwamnatin Zamfara.
Suna ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce da kuma rera waƙoƙin zanga-zanga, inda suke buƙatar gwamnati ta gaggauta kawo ƙarshen kashe-kashe da sace-sacen da ke addabar yankunansu.
A cewar masu zanga-zangar, ƙauyuka irin su Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka da Fegin Mahe sun zama wuraren kai hare-hare, inda mutane ke rasa rayukansu ko kuma a sace su kusan kowace rana.
Sun kuma koka da cewa ba su iya zuwa gonaki tun farkon damina saboda hare-haren, suna masu cewa ƴan bindigan ba wai kawai suna kashe mutane da sace su ba ne, har ma suna kwashe dukiya da lalata abinci.
Wani mai zanga-zanga mai suna Abubakar Abdullahi daga Fegin Mahe ya bayyana cewa ya rasa ƴan uwa da dama a sakamakon hare-haren ƴan bindiga.
A matsayinsa na manomi kuma ɗan kasuwa, ya ce ya yi asarar kayan da darajarsu ta haura N1m, ciki har da buhunan takin zamani da aka sace daga shagonsa yayin wani hari.
"Mun yi kuka mun gaji. Ƙauyukanmu suna cikin haɗari, kuma ba wani jami’in gwamnati da ya zo ya jajanta mana tun da rikicin ya tsananta kusan watanni uku da suka gabata."
- Abubakar Abdullahi
Da dama daga cikin masu zanga-zangar sun ce ba za su koma gida ba sai gwamnati ta biya buƙatunsu, rahoton The Punch ya tabbatar.

Source: Twitter
Me gwamnati ta fada musu
A martanin da ya mayar kan zanga-zangar, shugaban ƙaramar hukumar Gusau, Hon. Abubakar Iman ta bakin wakilinsa, Aminu Wakili Mada ya tabbatar da cewa sun ji koke-koken jama’ar Mada, Ruwan Bore da Fegin Mahe.
Ya tabbatar da cewa gwamnati tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro na aiki tukuru don dawo da zaman lafiya, kuma za su tura jami’an tsaro zuwa wuraren da abin ya fi shafa nan bada jimawa ba.
Ƴan bindiga sun kashe manoma a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasuu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun hallaka wasu manoma a hare-haren da suka kai a ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Bakura.
Miyagun sun riƙa bi ƙauye bayan ƙauye suna aikata ta'addanci kan mutanen d aba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


