Bidiyo: Shugaban Majalisa Ya Yi Suɓutar Baki, Ya Tura Tinubu 'Lahira' maimakon Buhari

Bidiyo: Shugaban Majalisa Ya Yi Suɓutar Baki, Ya Tura Tinubu 'Lahira' maimakon Buhari

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi subutar baki yayin jawabi kan karamci da girmamawar da aka yi a jana'izar Muhammadu Buhari
  • Akpabio ya yi kuskuren cewa Najeriya ta ji daɗin yadda gwamnati mai ci ta karrama tare da nuna girmamawa yayin jana'izar Tinubu maimakon Buhari
  • Sai dai nan take aka ankarar da shi kuskuren da ya yi kuma ya gyara, sannan ya ba da haƙuri, ya ci gaba da jawabin kan rasuwar tsohon shugaban kasar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi subutar baki yayin da yake bayani kan jana'izar ƙasa ta girmamawa da aka yiwa Muhammadu Buhari.

Sanata Akpabio ya yi kuskuren cewa 'jana'izar' Shugaba Bola Ahmed Tinubu maimakon Shugaba Buhari a zaman Majalisar Dattawa na yau Laraba.

Kara karanta wannan

Buhari: Majalisar dattawa ta shirya karrama tsohon shugaban kasa

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Shugaban Majalisar Dattawa ya yi subutar baki, ya ambaci Tinubu maimakon Buhari Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

AIT ta wallafa bidiyon wannan kuskure da shugaban majalisar ya tafka a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Dattawa ta girmama Muhammadu Buhari

A zaman yau Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025, Majalisar Dattawan Najeriya ta karrama marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Majalisar ta yi shirun minti ɗaya domin nuna girmamawa ga marigayin, wanda Allah ya yiwa rasuwa ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025 a wani asibiti a birnin Landan.

Bayan sanar da rasuwarsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima domin ɗauko gawarsa zuwa Daura.

Yadda Tinubu ya girmama marigayi Buhari

Shugaban bai tsaya iya nan ba, ya tafi jihar Katsina ya karbi gawar Buhari da kansa, aka yi wa marigayin faretin girmamawa a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'adua.

Daga nan kuma aka wuce mahaifarsa Daura, inda aka yiwa Buhari sutura kuma aka birne shi cikin girmamamwa a gidansa ranar Talata, 15 ga watan Yuli, 2025, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda Kiristoci suka yi wa Buhari addu'a a babban cocin kasa na Abuja

Wannan karramawa da gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta yi wa Muhammadu Buhari ta ƙayatar da ƴan Najeriya da dama.

Sanata Godawill Akpabio da marigayi Muhammadu Buhari.
Shugaban Majalisar Dattawa ya ba da haƙuri bayan ya yi suɓutar baki Hoto: @NGRSenate, Muhammadu Buhari
Source: Getty Images

Sanata Akpabio ya yi suɓutar baki a Majalisa

Da yake jawabi a zaman Majalisar Dattawa na yau Laraba, Sanata Akpabio ya ce jama'a sun ji daɗin abin da Gwamnatin Tinubu ta yi na girmama Buhari.

Yayin da zai ambaci yadda ƴan Najeriya suka yaba da jana'izar girmamawa da aka shiryawa Buhari, Sanata Akpabio ya yi subutar baki, ya ce "jana'izar Tinubu.

Akpabio ya yi subutar baki da cewa:

"Gaba ɗaya kasa ta yi farin ciki da abin da wannan gwamnati ta yi na karamci da girmamawa yayin jana'izar Shugaba Tinubu," amma nan take aka ankarar da shi ya gyara da cewa, "A yi hakuri, yadda aka karrama Buhari kuma aka birne shi."

Gwamna Sule ya ƙara karrama Buhari

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya sanya wa sabon titin Shendam sunan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari domin girmamawa.

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya," ADC ta tona abin da gwamnatin Tinubu ta yi a rasuwar Buhari

Abdullahi Sule ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta gabatar da kudirin doka a gaban majalisar dokokin Nasarawa domin samun goyon baya kan sauya sunan titin.

Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa girmamawar da ya nuna wa tsohon shugaban bayan rasuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262