MTN, Airtel, Glo da Sauran Kamfanonin Sadarwa Sun Yi Gargaɗi, Za a Iya Ɗauke Sabis a Jihohi 16
- Kamfanonin sadarwa da ke aiki a Najeriya sun roƙi hukumomin tsaro su kare kayan aikinsu daga hare-haren miyagu
- Sun yi gargaɗin cewa matukar aka ci gaba da kai hare-hare tare da sace kayayyakinsu, za a fuskanci tangarɗar hanyoyin sadarwa
- Kungiyar ALTON ta jero jihohin da lamarin ya fi muni, inda ta buƙaci a ƴan Najeriya su taimaka wajen kare turakan sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun yi gargaɗim cewa za a samu matsalar sabis a jihohi da dama cikin 'yan kwanaki masu zuwa idan hukumomin tsaro ba su ɗauki mataki ba.
Kamfanonin sun buƙaci dakarun tsaron Najeriya su taimaka wajen kare turakan sadarwa domin gujewa rashin karfin intanet da ɗaukewar sabis a wasu yankuna.

Source: Getty Images
A rahoton Vanguard, kamfanonin da suka ƙunshi MTN, Airtel da sauransu sun ce idan aka bar bara gurbi suna sace kayan sadarwa, ayyukan bangarori da dama zai gamu da cikas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yiwuwar a fuskanci matsalar sabis a Najeriya
Ɓangarorin da matsalar rashin sabis za ta fi shafa sun haɗa da banki, ilimi, ayyukan tsaro, waɗanda ke dogaro sosai da sadarwa.
Haka kuma ƴan Najeriya da ke amfani layin waya da intanet don shiga kafafen sada zumunta ko kiran waya, za su fuskanci matsala.
Wasu daga cikin wakilan kamfanonin sadarwa sun ce sun zuba jari sosai wajen inganta tsarin sadarwarsu, musamman bayan Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta amince da ƙaramin ƙarin farashi.
Amma, sun ce satar kayan aiki da lalata cibiyoyin sadarwa da wasu ke yi tare da gazawar hukumomin tsaro wajen dakile hakan ya raunana ƙarfin sabis da sauran ayyukansu.
Kamfanonin sadarwa sun koka kan hare-hare
Ƙungiyar manyan kamfanonin sadarwa ta kasa wato ALTON, ta nuna damuwa ƙwarai kan yadda sata da lalata kayayyakin sadarwa ke ƙaruwa a fadin Najeriya.
A cikin sanarwar da Shugaban ALTON, Injiniya Gbenga Adebayo, da Sakataren Yaɗa Labarai Damian Udeh suka rattaba hannu, ƙungiyar ce:

Kara karanta wannan
ADC: Atiku, Peter Obi da Amaechi sun cimma matsaya kan wanda zai yi takara a 2027
“Tun bayan goyon bayan da gwamnatin tarayya ta ba mu a farkon 2025, kamfanonin sadarwa sun zuba jari sosai wajen inganta hanyoyin sadarwa da ƙara ƙarfinsu.”
“Amma daga watan Mayu zuwa Yuli 2025, an sace da lalata cibiyoyin sadarwa a jihohin Ribas, Ogun, Osun, Imo, Kogi, Ekiti, Legas, Abuja da wasu jihohi da dama.”
"Muna cikin tsananin damuwa da yaduwar waɗannan hare-hare. Jihohin da abin ya fi muni sun haɗa da Delta, Ribas, Kuros Riba, Akwa Ibom, Ogun, Ondo, Edo, Legas, Kogi, Abuja, Kaduna, Neja, Osun da Kwara."

Source: Getty Images
ALTON ta aika saƙo ga hukumomin tsaro
Ƙungiyar ALTON ta ƙara da cewa hare-haren sun haifar da yawan katsewar layi, cunkoso a hanyoyin sadarwa, da tabarbarewar ingancin sabis, rahoton Tribune.
A ƙarshe, ta yi kira ga hukumomin tsaro tun daga ofishin mai ba da shawara kan tsaro da sauransu, da ƴan Najeriya su taimaka wajen kare hanyoyin sadarwa don kaucewa ɗaukewa ko tangarɗar sabis.
Ƴan Najeriya sun fara nuna danuwa kan tangarɗar sabis, Abdulhafiz Tukur ya shaida wa Legit Hausa sun jima suna fama da wannan matsala a yankin Ɗanta, jihar Katsina.
Ya ce tun wani lokaci da gwamnati ta sa aka ɗauke sabis gaba ɗaya saboda matsalar tsaro a wasu ƙananan hukumomin Katsina, har yanzu bai dawo daidai ba.
"Mun jima muna fama da matsalar rashin ƙarfi ko ɗauke war sabis har mun saba. Ina ganin tun da Masari ya sa aka ɗauke mana sabis saboda matsalar tsaro har yau be dawo daidai ba.
"Ya kamata kamfanonin sadarwa su gyara aikinsu gaskiya, musamman lokacin damina da muke ciki, ana samun matsala sosai," in ji shi.
Gwamnati ta amince da ƙarin kudin kira
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ya amince kamfanonin sadarwa su ƙara kudin kira, sayen data da tura saƙonni.
Ministan sadarwa na Najeriya, Bosun Tijani ya ce za a yi ƙarin kudin kira amma ba zai kai kaso 100% ba kamar yadda kamfanoni suka nema.
Bosun Tijani ya ce NCC za ta fitar karin da za a yi cikin adalci, tare da kare masu amfani da layukan sadarwa daga tsadar da ba za su iya dauka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

