'Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Zamfara, an Rasa Rayuka
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Zamfara
- Ƴan bindigan sun hallaka manoma da ke tsaka da bakin aiki bayan sun farmake su a ƙaramar hukumar Bakura
- Hazakalika, tsagerun sun kuma sace dabbobi masu yawan gaske bayan sun farmaki ƙauyuka guda uku
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun hallaka aƙalla manoma huɗu tare da sace dabbobi a wasu hare-hare da aka kai a jihar Zamfara
Ƴan bindigan sun hallaka manoman ne a yankin Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta jihar Zamfara, sakamakon jerin hare-haren da suka kai.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara
An samu rahoton cewa hare-haren, waɗanda suka faru a ranar Litinin, 21 ga watan Yulin 2025, wasu gungun ƴan bindiga fiye da 60 waɗanda ke tafe a kan babura suka kai su.
Maharan sun fara kai farmaki garin Damri da misalin ƙarfe 11:00 na safe, inda suka kai hari kai tsaye kan manoma da ke aiki a gonakinsu.
Wani manomi da ya tsira daga harin, Alhaji Shehu Maikasuwa ya bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne kawai kwatsam.
"Sun zo ne kwatsam, suka fara harbi, kowa ya fara guje-guje. Mutane biyu aka harba kuma sun samu munanan raunuka."
- Alhaji Shehu Maikasuwa
Daga bisani a wannan ranar, da misalin ƙarfe 5:45 na yamma, ƴan bindigan sun sake dawowa cikin rashin imani, inda suka kai farmaki lokaci guda a ƙauyuka uku na Turmi, Zugudum da Gidan Begu.
Dawowar ƴan bindigan ta haifar da mutuwar mutane huɗu da kuma satar shanu da ba a bayyana adadinsu ba.

Kara karanta wannan
Jirgin Sojin Sama ya rufto kan makaranta ana cikin karatu, mutane da dama sun mutu
Jami'an tsaro sun kai ɗauki
Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma, rundunar ƴan sanda, jami’an rundunar Askarawan Zamfara (CPG), mafarauta da ƴan sa-kai sun garzaya zuwa yankunan da aka kai harin domin kai ɗauki.

Source: Original
Wata majiya daga hukumomin tsaro ta bayyana cewa kafin isar jami'an tsaro, ƴan bindigan sun tsere daga yankunan bayan sun tafka ta'asa.
“Abin takaici, kafin jami’an tsaro su isa wurin da abin ya faru, ƴan bindigan sun riga sun tsere."
- Wata majiya
Majiyar ta ƙara da cewa an ciro gawarwakin waɗanda suka mutu, likitoci suka duba su sannan aka mika su ga iyalansu domin jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Hakazalika an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci mafi kusa don samun kulawa.
Ƴan bindiga sun harbi shugaban PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mummunan harin ƴan bindiga ya ritsa da wani shugaban jam'iyyar PDP a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun bude wuta ne kan shugaban PDP na ƙaramar hukumar Bukkuyum tare da muƙarrabansa.
A yayin harin dai an raunata shugaban na PDP yayin da sauran muƙarrabansa suka samu munanan raunuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
