An Kama Masu Garkuwa 13 Hannu da Hannu bayan Gwabza Fada da Jami'an Tsaro
- An kama mutum 13 da ake zargi da garkuwa da mutane da bayar da bayanai a wani samame na hadin gwiwa tsakanin Kogi da Kwara
- Jami’an tsaro daga ofishin NSA da sauransu ne suka gudanar da samamen a yankunan Yagba da Patigi da Gbugbu
- Wasu daga cikin masu garkuwan sun tsere yayin da wasu mata da aka sace suka samu kubuta, kuma an jikkata jami’in tsaro daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi – Gwamnatin Jihar Kogi ta tabbatar da cafke wasu mutum 13 da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane da kuma bayar da bayanai ga masu laifi a wani samame.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Fanwo ya ce hadin gwiwa da jami'an tsaro na jihohin Kogi da Kwara ne ya kai ga wannan nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fanwo ya ce an gudanar da samamen ne a Isanlu-Esa da Okoloke a Karamar Hukumar Yagba ta Yamma da ke Jihar Kogi, da kuma Patigi, Lafiagi da Gbugbu da ke Jihar Kwara.
Sunayen wadanda hukuma ta kama
Fanwo ya bayyana sunayen wadanda aka kama bisa zargin yin garkuwa da mutane sun hada da Mainasara Abubakar, Sadik Abubakar, Jude Sani.
Baya ga haka akwai Sanda Abubakar, Lawali Usman, Tukur Shehu, Hassan Abubakar, Kabiru Surajo, Makiri Dodo, Bala Hassan, Umaru Sanda da Ruwa Abubakar.
Sannan kuma ya ce an kama wani mutum mai suna Rabiu Makeri da ake zargin yana bayar da bayanai ga masu garkuwa da mutane a yankin.
Yadda jami'an suka gudanar da samamen
Jami’an tsaron sun fafata da wadanda ake zargin a wani artabu mai zafi, inda wasu daga cikin su suka tsere, suka bar babura da wadanda suka yi garkuwa da su.
An ce an kubutar da mata da dama da aka sace yayin artabun, yayin da wani jami’in tsaro ya jikkata kuma yanzu haka yana karbar magani a asibiti a Yagba.
Martanin gwamnatin jihar Kogi
Kwamishinan yada labaran ya jinjinawa jami’an tsaron ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da sauran jami’ai kan jajircewarsu da kuma kokarinsu.
Ya kuma bayyana godiya ga gwamnatin Jihar Kwara bisa hadin kai da taimako da ta bayar wajen cimma wannan nasara, yana mai cewa lamarin ya dawo da zaman lafiya a Kogi ta Yamma.

Source: Facebook
Kwamishinan ya kara da cewa Gwamna Ahmed Usman Ododo ya dauki alhakin sayen magani da jinyar jami’in tsaron da ya jikkata.
Ya ce:
“Akwai tabbaci cewa wadanda aka kama za su fuskanci shari’a bayan kammala bincike, domin gwamnatin jihar ba za ta lamunci aikata laifi ba.”
An kai wa makiyaya hari a jihar Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari cikin dare kan Fulani makiyaya a jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki Fulanin ne dauke da manyan makamai kuma sun sace shanu da dama.
Jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji sun shiga daji domin ceto shanun da kuma kama maharan da suka kai harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

