'Kwankwaso ne Zai Maye Gurbin Buhari', Jigon NNPP Ya Fadi Dalili
- Jigo a jam'iyyar NNPP ya bayyana Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan siyasan da zai iya maye gurbin Muhammadu Buhari
- Alhaji Aminu Ringim ya bayyana cewa Kwankwaso yana da wasu halaye da ɗabi'u irin na marigayi tsohon shugaban ƙasan
- Tsohon 'dan takaran gwamnan ya amince cewa cike gurbin da Buhari wanda ya rasu a Landan, ya bari ba abu ba ne mai sauƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar NNPP Alhaji Aminu Ringim, ya faɗi ɗan siyasan da zai iya maye gurbin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Alhaji Aminu Ringim ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ne kaɗai ɗan siyasa da zai iya maye gurbin marigayi Buhari.

Source: Twitter
Alhaji Aminu Ringim ya faɗi hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Kwankwaso zai iya maye gurbin Buhari?
Ya bayyana ayyukan Kwankwaso wajen ci gaban ɗan adam da samar da ababen more rayuwa a lokacin da yake gwamnan Kano a matsayin dalilinsa na samun wannan matsaya.
Ya daidaita Kwankwaso da fitattun jagororin Arewa kamar Sir Ahmadu Bello da Malam Aminu Kano waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen kare talakawa.
"Tabbas giɓin da Buhari ya bari ba mai sauƙin cikewa ba ne, amma idan akwai wani a cikin ƴan siyasar Najeriya da ke ɗauke da amana, ƙanƙantar kai da ƙaunar talakawa irin na Buhari, to babu wanda ya kai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso."
“A tsawon shekaru, Kwankwaso ya tabbatar da kansa a matsayin ɗan siyasa mai mutane. Yana rayuwa tare da jama’a, yana magana da harshensu, kuma yana fahimtar buƙatunsu."
"Kudirinsa kan ilimi, samar da abin yi ga matasa da adalci a zamantakewa ya daidaita da tafiyar marigayi Buhari."
- Alhaji Aminu Ringim
'Kwankwaso na da magoya baya' - Ringim
Ya ƙara da cewa Kwankwaso bai fito a matsayin ɗan siyasa na masu hannu da shuni ba, sai dai mutum ne mai sauƙin kai, mai shiga talakawa kuma mai ƙoƙari wajen fitar da su daga fatara.
Jigon na NNPP ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kano shine ɗan siyasa da ya fi kusanci da falsafar Aminu Kano ta hidimtawa talakawa.

Source: Facebook
Alhaji Aminu Ringim ya ƙara da cewa Kwankwaso yana da tasiri a siyasa har fiye da jihar Kano, inda ya ce yana da magoya baya a jihohin Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto, Kebbi har ma da wasu sassa na Arewa ta Tsakiya.
"Abin da ya bambanta shi da saura shi ne, kwarjininsa ya wuce addini, ƙabila. Ba kawai gwarzon Arewa ba ne, amma mutum ne da ke kan hanyar zama jajirtaccen dattijon ƙasa."
- Alhaji Aminu Ringim
Tsohon 'dan takaran gwamnan ya yi watsi da masu ƙoƙarin takaita Kwankwaso ga siyasar jiha ko yanki, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙaramar fahimta da ba ta dace da tasirinsa a fagen siyasa ba.
Wani masoyin Buhari ya shaidawa Legit Hausa cewa a 'yan siyasan da ake da su a yanzu, babu wanda zai iya maye gurbin tsohon shugaban kasan.
Kabir Magaji ya bayyana cewa Buhari sai an dade kafin a samu irinsa ko wanda zai maye gurbinsa.
"Ba mu sani ba dai ko nan gaba, amma a yanzu dai babu wanda zai iya maye gurbin Muhammadu Buhari."
"Kwankwaso yana da mutane da tasiri irin na sa, amma ko kadan bai kama kafar Buhari ba."
- Kabir Magaji
Majalisa za ta karrama Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta shirya karrama tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Majalisar za ta karrama marigayin ta hanyar wani zama na musamman da ta shirya a ranar Laraba, 24 ga watan Yulin 2025.
Karrama tsohon shugaban ƙasan na zuwa ne bayan rasuwarsa a wani asibiti a birnin Landan a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


