Buhari: Majalisar Dattawa Ta Shirya Karrama Tsohon Shugaban Kasa

Buhari: Majalisar Dattawa Ta Shirya Karrama Tsohon Shugaban Kasa

  • Majalisar dattawan Najeriya ta yanke shawarar karrama tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya riga mu gidan gaskiya
  • An amince da gudanar da zama na musamman a majalisar don karrama Buhari wanda ya rasu a birnin Landan sakamakon rashin lafiya
  • Majalisar dattawan za ta gudanar da zaman ne bayan da majalisar zartaswa ta tarayya ta yi irinsa a makon da ya gabata

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta shirya karrama tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari.

Majalisar dattawan za ta gudanar da zama na musamman a ranar Laraba domin karrama marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Majalisar dattawa za ta karrama Buhari
Majalisar dattawa ta shirya karrama Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta rahoto cewa majalisar ta cimma wannan matsayar ne yayin zamanta na ranar Talata, 22 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Buhari dai ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan, bayan ya yi jinyar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

UNIMAID: An faɗi babban dalilin da ya sa Tinubu ya sauya sunan jami'a saboda Buhari

An birne marigayi tsohon shugaban ƙasan a gidansa da ke Daura, jihar Katsina, a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.

Yaushe majalisa za ta karrama Buhari?

An yanke shawarar gudanar da zaman ne a ranar Talata bayan wani ƙuduri da Sanata Gbenga Daniel, wanda ke wakiltar Ogun ta gabas, ya gabatar domin girmama Awujale na Ijebu, marigayi Oba Sikiru Adetona.

Sarki Sikiru Adetona ya rasu ne awanni kaɗan bayan sanar da rasuwar Buhari, wanda yake abokinsa ne na dogon lokaci.

Majalisar ta yi shiru na minti guda domin tunawa da marigayi sarkin.

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce ƙasar nan ta yi babban rashi na fitattun ƴaƴanta biyu a rana ɗaya.

"Don tunatarwa, shugaban majalisa da abokan aikina masu girma, Najeriya ta yi rashin wasu ƴaƴanta guda biyu masu daraja a rana ɗaya. Na biyu kuwa shi ne mai girma, tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, GCFR."
“Ina son sanar da cewa, da ikon Allah, gobe Laraba, majalisar dattawa za ta ɗauki wani ƙuduri na musamman domin girmama marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, kuma abokan aikina za su samu damar ba da ta su gudunmawar."

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

- Opeyemi Bamidele

Ya bayyana cewa wannan zaman karramawar zai kasance domin tunawa da tarihin marigayin da gudunmawar da ya bayar ga ci gaban ƙasa bayan rasuwarsa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Majalisar dattawa za ta karrama Buhari
Majalisar dattawa za ta yi zama na musamman saboda Buhari Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Buhari na samun karramawa

A makon da ya gabata, majalisar zartaswa ta tarayya ta gudanar da zama na musamman domin karrama marigayi tsohon shugaban ƙasan

Buhari ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan daga baya ya zama shugaban ƙasa na farar hula daga 2015 zuwa 2023.

Gwamnan Nasarawa ya karrama Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya karrama tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Gwamna Sule ya sanyawa sabon titin Shendam da aka gama ginawa sunan Muhammadu Buhari domin girmama da mutunta shi.

Ya bayyana cewa ya sanya sunan marigayi tsohon shugaban ƙasan na Najeriya ne domin a riƙa tunawa da shi na tsawon lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng