Jerin Wuraren da aka Sanya wa Sunan Marigayi Muhammadu Buhari a Najeriya
Bayan rasuwar shugaba Muhammadu Buhari, gwamnatin Bola Tinubu ta dauki matakan girmama shi ciki har da sauya sunan jami'ar Maidiguri zuwa sunan shi.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - A ranar 13 ga Yuni Allah ya karbi rayuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a London.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan jami'ar Maiduguri zuwa jami'ar Muhammadu Buhari saboda girmama shi.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun kawo muku wasu muhimman wurare da aka sanya wa sunan shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Jami'ar Muhammadu Buhari, Maiduguri
Ma’aikatar Ilimi ta bayyana cewa an sanya wa Jami’ar Maiduguri sunan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne sakamakon jajircewarsa wajen bunkasa ilimi.
Punch ta wallafa cewa, daraktar yada labarai ta ma’aikatar ilimi, Folasade Boriowo ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
A cewar sanarwar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da sauya sunan yayin wani taro na musamman na majalisar zartaswa ta tarayya da aka gudanar domin girmama marigayi Buhari.
Shugaban kasar ya bayyana Buhari a matsayin dattijo wanda gwamnatinsa ta bai wa tsaron kasa, farfado da tattalin arziki, gyaran hukumomi da yaki da cin hanci muhimmanci.

Source: Twitter
2. Rukunin gidajen Buhari a Gombe
A jihar Gombe, an sanya wa wata unguwa da aka gina rukunin gidaje masu yawa sunan Muhammadu Buhari.
Bayan gina gidajen da tsawon shekaru, gwamnatin jihar Gombe ta samar da makaranta a unguwar kuma ita ma an jingina mata sunan Muhammadu Buhari.

Source: Original
Shugaban kungiyar tsofaffin daliban makarantar, Muhammad Babayo Aliyu ya bayyana cewa Legit cewa an dade da gina rukunin gidajen kafin a bude makarantar.
Babayo ya ce:
"An bude karamar makarantar sakandare ta jeka-ka-dawo ne a wajen a ranar 4 ga Oktoba a shekarar 2007"
Baya ga haka, akwai makarantar firamaren Muhammadu Buhari a wajen."
3. Gandun masana'antun Buhari a Gombe
Filin Masana'antu na Muhammadu Buhari wani katafaren aiki ne mai fadin hekta 1,000 da ke hanyar Dadin Kowa a Jihar Gombe, Najeriya.
Wurin na da nufin karfafa masana'antu, samar da guraben ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arziki a Gombe da yankin Arewa maso Gabas gaba daya.
An tanadi muhimman abubuwa a filin kamar hanyoyi, wutar lantarki, da kuma ruwa domin amfanin yau da kullum.
Tribune ta rahoto cewa kamfanoni da dama sun fara gina masana’antunsu a ciki ko kuma suna aiki a wajen, sannan an riga an karɓi sama da buƙatu 400 daga masu sha’awar samun fili a ciki.

Source: Facebook
4. Hanyar Buhari a jihar Nasarawa
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sauya sunan titin Shendam da aka kammala kwanan nan, ya sanya masa sunan marigayi Muhammadu Buhari.
Sabon titin mai layi biyu da aka gina, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya kaddamar da shi a lokacin ziyarar yini guda da ya kai jihar a karshen watan da ya gabata.
Legit ta rahoto gwamna Sule ya ce sauya sunan wannan muhimmin titi wata hanya ce ta girmama wa da kuma tunawa da tsohon shugaban kasar.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tura daftarin kudiri zuwa majalisa domin samar da goyon bayan doka wajen sauya sunan titin daga hanyar Shendam zuwa Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
5. Filin jirgin saman Muhammadu Buhari
A 2023, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta umurci Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da ta sake sunayen wasu filayen jiragen sama na tarayya domin girmama fitattun mutane.
Punch ta wallafa cewa hukumar FAAN ta fitar da sanarwar haka ne a wata wasika da aka rubuta a ranar 1 ga Yuni, 2023.
A cikin bayanin da hukumar ta fitar, an sake wa filin jirgin saman Maiduguri suna, inda aka rada masa sunan Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
Dangin Buhari sun yi godiya wa jama'a
A wani rahoton, kun ji cewa, dangin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun fito sun yi godiya bayan kammala zaman makoki.
Malam Mamman Daura ne ya yi magana a madadin dangin, inda ya yi godiya ta musamman ga Bola Tinubu da mataimakin shi, Kashim Shettima.
Mamman Daura ya jero sunayen mutane 34 da suka taka rawa wajen rashin lafiya da jana'izar tsohon shugaban kasar da ya rasu a London.
Asali: Legit.ng


