Sanata Natasha Ta Yi Raddi Mai Zafi ga Akpabio kan Hana Ta Shiga Majalisa

Sanata Natasha Ta Yi Raddi Mai Zafi ga Akpabio kan Hana Ta Shiga Majalisa

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gamu da cikas yayin da ta yi yunƙurin komawa kujerarta a majalisar dattawa
  • Jami'an tsaron da ke bakin aiki a majalisar dattawan sun hana ta shiga ciki domin komawa bakin aiki a ranar Talata
  • Biyo bayan hana ta shiga, Sanatar ta yi kalamai masu kaushi kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gargaɗi shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kan kada ya riƙa jin yafi kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sanatar ta kuma zargi shugabannin majalisar dattawa da take umarnin kotu ta hanyar hana ta dawowa bakin aikinta a majalisar tarayya.

Sanata Natasha ta ja kunnen Akpabio
Sanata Natasha ta gargadi Godswill Akpabio Hoto: Natasha H Akpoti, Godswill Obot Akpabio
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce ta bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a harabar majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An hana Sanata Natasha shiga majalisa

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun tare Sanata Natasha, sun hana ta shiga ofis a Majalisa

Sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta iso harabar majalisar tarayya domin komawa kan kujerarta, biyo bayan hukuncin da mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya ta yanke, wanda ya soke dakatarwar da aka yi mata.

Sai dai jami’an tsaro da ke bakin ƙofa sun hana ta shiga cikin majalisar.

Yayin da take bayyana fushinta kan lamarin, Sanata Natasha ta bayyana abin da ya faru a matsayin keta umarnin kotu da gangan daga ɓangaren majalisar dattawa, musamman shugabanta, Godswill Akpabio.

Me Natasha ta ce kan Akpabio?

“Akpabio ba gaba yake da kundin tsarin mulki ba. Ina so ƴan Najeriya su sani cewa kujerar shugaban majalisar dattawa ba ita ce ke ba ni halaccin zama sanata ba."
"Ɗaukaka ƙarar da ya yi bai soke hukuncin da mai shari’a Binta Nyako ta yanke ba, kuma hakan bai hana ni ci gaba da kasancewa sanata ba."
“Ina da halaccin zama sanata ne daga jama’ar Kogi da suka zaɓe ni."

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanatar ta ce ci gaba da hana ta shiga majalisar na nuni da irin halin da dimokuraɗiyyar Najeriya ke ciki, rahoton TheCable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi bayani yayin da aka fara taron daidaita farashin fetur a Abuja

“An hana ni shiga majalisar tarayya, kuma wannan babban saƙo ne da ake aikawa. Ya zama tarihi cewa majalisar tarayya ƙarƙashin shugabancin Akpabio ta zaɓi yin kunnen uwar shegu da hukuncin kotu."

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Natasha ta yi kalamai kan Akpabio
Sanata Natasha ta gargadi Godswill Akpabio Hoto: Natasha H Akpoti, Nigerian Senate
Source: Facebook

Wane mataki Natasha za ta ɗauka?

Ta bayyana cewa lauyoyinta za su garzaya kotun daukaka ƙara domin neman ƙarin fassara da mafita kan lamarin.

"Abin da zan yi, zan gana da tawagar lauyoyina domin su shigar da ƙara zuwa kotun daukaka ƙara don neman ƙarin fassara kan abin da ya faru. Ni mai bin doka ce."

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Natasha ta sha alwashin komawa majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta sha alwashin komawa kan kujerarta.

Sanata Natasha ta bayyana cewa za ta koma majalisa ne biyo bayan hukuncin kotu wanda ya soke dakatarwar da aka yi mata.

Ta bayyana cewa tuni ta sanar da shugabannin majalisar shirinta na dawowa bakin aiki domin ci gaba da wakiltar mutanen ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng