Gwamnoni 3 da Sarkin Kano Za Su Halarci Muhimmin Taron Musulunci na Kwana 2
- Makarantar Al-Faidiyyah mai koyar da ilimin addinin musulunci da Larabci ta shirya bikin cika shekaru 60 da kafuwa a Legas
- Bikin wanda zai shafe kwanaki biyu, ana sa ran zai samu halartar manyan baki ciki har da gwamnonin Kano, Katsina da Neja
- Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II na cikin sarakunan da ake sa ran ganinsu a wannan taro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legas - Gwamnonin jihohin Kano, Neja da Katsina na daga cikin manyan baki da ake sa ran za su halarci bikin cika shekaru 60 da kafuwar Makarantar Al-Faidiyyah ta Karatun Larabci da Addinin Musulunci a Lagos.
Gwamnonin da suka haɗa da Alhaji Abba Kabir Yusuf (Kano), Mohammed Umar Bago (Neja) da Dikko Umar Radda (Katsina) za su halarci wannan taro na musulunci.

Source: Original
A cewar masu shirya taron, wannan bikin zai gudana na tsawon kwanaki biyu, daga 26 zuwa 27 ga watan Yuli 2025, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Kano zai haɗu da gwamnoni 3 a Legas
Ana sa ran taron zai sami halartar manyan sarakuna kamar Oba Rilwan Akiolu na Lagos, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Haka zalika za a ga Farfesa Ibrahim Ahmad Makari, Babban Limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
An kafa makarantar shekaru 60 da suka wuce ta hannun marigayi Sheikh Imam Mukhtar Danlami, ta shahara a matsayin jagora kuma fitacciyar cibiyar ilimin addini musamman a tsakanin Hausawa da ke kudancin Najeriya.
A bana, makarantar za ta yaye dalibai kusan 120 waɗanda suka kware wajen karatun Al-ƙur’ani kuma suka kammala matakin ilimin firamare.
Dalilin kafa makarantar Al-Faidiyyah
Musa Ibn-Saidu, mataimakin shugaban kungiyar iyaye da malamai ta makarantar (PTA), ya jaddada muhimmancin ilimin addinin musulunci da na Larabci a cikin al’umma.

Kara karanta wannan
Batan maciji ya birkita ƴan Kano, Sanusi II ya roƙi kwamishinan ƴan sanda alfarma
“Nan unguwar Agege ce, yankin da ke da yawan jama’a a Lagos. Yara da dama ba sa zuwa makarantar zamani.
"Abin da kawai za mu iya yi don taimaka musu shi ne mu kawo su nan, mu koya musu ilimi kuma mu hana su yawon banza a titi, ta haka muna rage aikata munanan dabi’u,” in ji shi.

Source: Facebook
Wace gudummuwa makarantar take bayar wa?
Ya bayyana cewa idan ba a tura matasa makaranta ba, suna iya fadawa cikin mummunar mu’amala da abokai, wanda hakan na iya jawo su shiga amfani da miyagun kwayoyi, sata da sauran laifuffuka.
"Rashin aikin yi ko rashin sanya su a makaranta yana iya jawo wa jiha matsala. Yanzu da wayoyin zamani ke yawo, kowanne yaro na so ya mallaki wayar salula, amma ba sa yin halastattun abubuwa da su.
"Saboda haka, ta hanyar wannan ilimin da muke bayarwa a araha, za mu iya hana su zaman banza a titi, sannan bayan makaranta mu taimaka musu da ayyuka da za su rika yi, don rage zaman banza.
- Inji Musa Ibn-Saidu.
Sanusi II ya buɗe sabon masallacin Juma'a a Kano
A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya jagoranci bude sabon masallacin Jumu’a a Zawaciki da ke jihar Kano.
Mai Martaba Sarkin ya yi limancin Juma'a ta farko a sabon masallacin, inda ya yi huɗuba a ranar 18 ga watan Yuli, 2025.
Masarautar Kano, a wata sanarwa da ta fitar bayan buɗe masallacin, ta bayyana cewa an sanya wa sabon wurin iɓadar suna, 'masallacin Al-ansar Wal Muhajirun'.
Asali: Legit.ng

