'Ku Shirya': Kano, Bayelsa da Jihohi 33 da za a Sheka Ruwa da Iska Mai Karfi

'Ku Shirya': Kano, Bayelsa da Jihohi 33 da za a Sheka Ruwa da Iska Mai Karfi

  • NiMet ta yi gargaɗi game da yiwuwar saukar ruwan sama da iska mai ƙarfi da ka iya janyo ambaliya a sassa da dama na ƙasar nan
  • Hukumar ta bayyana cewa jihohin Arewa kamar su Adamawa, Taraba za su sha ruwan sama mai ƙarfi da tsawa da safiyar Talata
  • A bangaren Kudancin Najeriya kuwa, Cross River, Rivers, Delta da Bayelsa za su fara shan ruwan sama tun da safe har zuwa dare

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na yau Talata, 22 ga Yulin 2025.

NiMet ta bayyana cewa akwai yiwuwar a samu saukar ruwan sama mai karfi hade da tsawa a jihohi daban-daban na ƙasar.

NiMet ta hango ruwan sama hade da tsawa da iska mai karfi a sassan Najeriya ranar Talat
Ana sheka ruwan sama tare da tsawa a wasu sassan Arewacin Najeriya, Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Hasashen yanayi a Arewacin Najeriya

A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na X a yammacin Litinin, NiMet ta yi hasashen cewa:

Kara karanta wannan

Tanka makare da fetur ta yi hatsari, ta kama da wuta kusa da gidan man NNPCL

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ana sa ran ruwan sama mai ƙarfi tare da tsawa zai sauka a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Borno, Yobe, Gombe, Jigawa, Bauchi, da Kaduna da safiyar Talata.
"Daga yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Zamfara, Sokoto, Taraba, Bauchi, Kano, Katsina, Kebbi, Kaduna, Borno, Gombe, da Adamawa."

A shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta yi hasashen ruwan sama zai sauka ne a sassan jihohin Neja, Kwara, Kogi, da Benuwe da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT) da safiyar Talata.

Da yammaci zuwa dare kuma, ana sa ran ruwan sama mai karfi zuwa matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Plateau, Nasarawa, FCT, Kogi, Benuwe, da Neja.

Hasashen yanayi a jihohin Kudu

Da Safiyar Talata, hukumar NiMet ta yi hasashen samun hadari amma da hudar rana a faɗin yankin Kudancin Najeriya.

Amma NiMet ta ce akwai yiwuwar samun ruwan sama da safe a sassan jihohin Cross River, Akwa Ibom, Rivers, da Bayelsa.

Kara karanta wannan

Za a sheka ruwa da tsawa na kwana 3 a Abuja, Kano da jihohin Arewa 18 daga Juma'a

Da yammaci kuwa, ana sa ran ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi zai sauka a sassan jihohin Imo, Anambra, Ebonyi, Enugu, Abia, Osun, Ekiti, Ondo, Oyo, Edo, Delta, Bayelsa, Legas, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom.

NiMet ta gargadi jihohin Arewa

Rahoton da NiMet ta fitar ya nuna mafi yawan jihohin Arewa na cikin launin ja, wanda ke nuna haɗarin iska mai ƙarfi da yiwuwar ambaliya.

A ranar Talata, ana sa ran zafin rana zai kai digiri 34°C a Kano da Katsina, yayin da Sokoto da Dutse za su fuskanci 33°C. A Bauchi da Gombe, ana sa ran ruwan sama da zafin rana na 31°C da 30°C.

Hukumar NiMet ta shawarci jama’a da cewa:

“Ruwan sama da tsawa na iya zuwa da iska mai ƙarfi; a kasance cikin shiri kuma a dauki matakan kariya. Direbobi su guji tukin mota a cikin ruwan sama mai yawa don kaucewa haɗura.”

Ta kuma gargadi mutane su guji fakewa a karkashin bishiyoyi yayin da ake ruwa da iska saboda haɗarin karyewar rassan bishiyoyi.

Hakazalika, NiMet ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayin filayen jirgi daga hukumar domin tsara tafiye-tafiyensu cikin aminci.

Kara karanta wannan

'Ku shirya': Yobe, Kano da jihohi 9 za su fuskanci ambaliyar ruwa daga ranar Lahadi

Duba sanarwar a nan kasa:

Jihohi 20 da za su fuskanci ambaliya a Yuli

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta gargadi jihohi 20 game da yiwuwar ambaliyar ruwa a watan Yuli 2025.

Hukumar ta bayyana Sokoto a matsayin jihar da ke cikin matsanancin haɗarin ambaliya, sai Kaduna, Zamfara, Yobe da wasu jihohi 16.

NiMet ta shawarci jama'a da su tsaftace magudanan ruwa, su guje wa tuki yayin da ake ruwa mai ƙarfi don kaucewa haɗari, da kuma yin kaura daga wuraren da ambaliya za ta shafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com