N Power: Matasa Sun Tuna da Buhari, an Maka Tinubu a Kotu kan Basukansu

N Power: Matasa Sun Tuna da Buhari, an Maka Tinubu a Kotu kan Basukansu

  • Matasan da suka amfana da shirin N-Power sun maka gwamnatin APC a kotu, suna neman diyyar N5bn da biyan kudaden da suke bi
  • Masu karar sun ce gwamnati ta ci amanar aiki, ta gaza biyan hakkokinsu duk da sun yi aikin da aka dauke su akai
  • Wasu daga cikinsu ya bayyana yadda rashin kudin ya durkusar da rayuwarsa, suna maraba da wannan matakin kotu da aka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Matasa da suka ci gajiyar shirin N-Power sun dauki matakin shari’a kan gwamnatin tarayya.

Matasan sun nuna damuwa da rashin biyansu kudaden alawus da suka tara na tsawon watanni.

An maka Tinubu a kotu kan basukan Npower
Matasan Npower sun maka Tinubu a kotu kan basuka. Hoto: Nentawe.
Source: Facebook

Masu karar na neman gwamnatin ta biya su N5b a matsayin diyya kan cin zarafi da tauye hakki, cewar rahoton Legit.ng.

Kara karanta wannan

An zargi gwamnati da hannu a watsar da aikin titin Kano zuwa Katsina, ana asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shari’ar ta samo asali ne daga matasan Najeriya da suka ce suna wakiltar sauran tsofaffin wadanda suka ji gajiyar shirin N-Power da gwamnatin ta dauka aiki.

Farkon fara shirin N-Power a gwamnatin Buhari

Shirin N-Power wani tsari ne da tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari ya kafa a watan Yunin 2016 don rage zaman banza.

A kalla matasa da suka amfana da shirin 230,000 ne suka gurfanar da gwamnatin APC a gaban babbar kotun masana’antu da ke Abuja.

Matasan suna karbar N30,000 duk wata na tsawon shekara guda, yayin da wadanda ba su da kwalin digiri ke karbar N10,000.

Dalilin maka Tinubu a kotu kan basukan N-Power
Matasan N-Power sun maka Tinubu a kotu kan basukan da suke bi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Sauran wadanda matasan N-Power ke kara

Wannan kara mai lamba NICN/ABJ/214/2025 na karkashin lauyoyi da A.A. Hikima ke jagoranta, ya kunshi mutane 10 a madadin 231,871.

Wadanda ake kara sun hada da ma’aikatar jin kai da walwala, ministan Shari'a, Akanta-janar da shugaban shirin N-Power.

Kara karanta wannan

APC ta sanya ranar gudanar da babban taro, ana neman magajin Ganduje

Sun ce tun da gwamnati ta dauke su aiki da suka yi da gaske, rashin biyansu ya zama zalunci da karya dokar kwadago.

Bukatun matasan N-Power a gaban kotu

A cikin takardun karar, suna neman kotu ta yanke cewa kin biyansu kudin alawus ya sabawa dokokin aiki da kundin tsarin mulki.

Sun kuma nemi kotu ta ayyana haka a matsayin rashin adalci da saba wa ka’idoji, suna son kotu ta umarci gwamnatin da ta biya duka kudaden da suke binta.

Sun kuma bukaci kotu ta tilasta gwamnati ta biya N5bn a matsayin diyya da kuma N50m na kudin shari’a, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.

N-Power: Martanin wani matashi a Gombe

Daya daga cikin waɗanda suka amfana, Sani Ahmad a Gombe, ya bayyana yadda rashin kudin ya shafi rayuwarsa da iyalinsa.

Ya ce:

“N-Power shi ne kawai abin da gwamnatin Najeriya ta taba bani tun da na kammala karatu a 2010.
“Na yi aikin koyarwa a wata makaranta kuma kudin alawus din ke taimaka min da iyalina.
“Amma kwatsam sai gwamnati ta daina biyana, na ci gaba da zuwa aiki da fatan za su biya amma babu wani abu."

Kara karanta wannan

Batan maciji ya birkita ƴan Kano, Sanusi II ya roƙi kwamishinan ƴan sanda alfarma

Ya ce ya karbi bashi domin cigaba da rayuwa, da fatan gwamnati za ta biya, amma har lokacin da Buhari ya sauka, ba a biya ba.

Tinubu ya umarci sauya fasalin N-Power

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya juyo ta kan shirin N-Power bayan dakatar da tsarin saboda zargin badakala kan tsohuwar Minista, Betta Edu.

Tinubu ya ba da umarnin sake fasalin shirin N-Power don ƙara inganta ayyukansa da tasirinsa ga rayuwar matasa.

An ware sama da kayayyaki 100,000 da kuma N32.7bn don tallafa wa matasa da marasa galihu, musamman mata da matasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.