Batan Maciji Ya Birkita Ƴan Kano, Sanusi II Ya Roƙi Kwamishinan Ƴan Sanda Alfarma
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bukaci 'yan sanda su binciki batan mesa da ake zargi a jihar
- Majiyoyi sun ce mesar ta bata da ake zargin mallakin tsohon Akanta-janar ne a Kano, wanda yanzu ya dawo gida
- Al’umma sun kai kuka gaban Sarki, suna korafi kan kiwon dabbobi masu hadari da ake yanka shanu don ciyar da su
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An shiga firgici a jihar Kano bayan tabbatar da batan maciji na wani tsohon Akanta-janar a jihar.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, da ya zurfafa bincike kan batan wata mesa.

Source: Twitter
Sanusi II ya nuna damuwa kan batan maciji
Mesar da ta kuɓce, ana zargin mallakin tsohon Akanta-Janar, Ahmed Idris ce, wadda ta shiga gari tare da haddasa fargaba a tsakanin jama’a, cewar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan korafi ya fito daga bakin al’ummar unguwar Daneji a karkashin jagorancin mai unguwa Malam Abba Lawan da suka ziyarci Sarki.
Sarkin ya bayyana damuwa kan kiwon dabbobi masu hadari a cikin gari da kuma yankan shanu domin ciyar da su a gidan tsohon Akantan.
Ya shawarci tsohon Akantan da ya gaggauta dauke dabbobin domin kaucewa hadurra da ka iya biyo baya muddin aka ci gaba da hakan.
Kalar dabbobi da tsohon Akanta-janar ke kiwo
A baya an samu rahotanni cewa tsohon Akantan yana kiwon zakuna, kada, macizai da mesa a gidansa inda ake yanka musu shanu a fili.
Mai unguwar, Malam Abba, ya bayyana cewa ya gana da tsohon Akantan kai tsaye yana fada masa hadarin dabbobin da ke cikin gidan.
Ya ce:
“Na fada masa cewa irin wadannan namun daji na da hatsari, sai ya ce zai dauke su, amma har yanzu bai dauke su ba."

Kara karanta wannan
'Zai yi wahala Obi ya yi shugaban kasa,' Hadimin Buhari ya yi martani ga Obidients

Source: Twitter
Kano: An kai korafi gaban Sarki Sanusi II
Bayan ya ga lamari bai canja ba, mai unguwa ya rubuta rahoto ya mikawa Wakilin Kudu, wanda ya mika zuwa Wakilin Hakimi har gaban Sarki.
A ranar Litinin suka ziyarci Sarki da korafi, inda aka karanta takarda a gabansa kuma ya umarci a kai wa ‘yan sanda don bincike, Kano Times ta tabbatar.
“Yau Litinin muka je gaban Sarki, yace a rubuta wa ‘yan sanda takarda a hukumance domin daukar mataki."
- Cewar Mai Unguwa.
Ya ce suna fatan takardar za ta isa ofishin kwamishinan ‘yan sanda a ranar Talata domin tabbatar da tsaro a unguwar Daneji.
Sanusi II ya magantu kan maza masu dukan mata
Kun ji cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nuna damuwa kan halayen wasu maza masu dukan matansu musamman a Arewacin Najeriya.
Sarkin ya ce Musulmi na gari ba ya dukan matarsa, kuma masu cin zarafin ba su fahimci addini ba ne ko kadan saboda Musulunci ya yi bayani kan matsalar.
Basaraken ya bayyana cewa malamai da limamai na da rawar da za su taka wajen sauya halayen al’umma cikin sauki da kawo karshen matsalar a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
