Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Hana Kananan Hukumomin Kano Samun Kudade

Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Hana Kananan Hukumomin Kano Samun Kudade

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yi hukunci kan buƙatar neman hana ba ƙananan hukumomi 44 na jihar kuɗaɗe daga asusun tarayya
  • Alƙalin kotun ya yi watsi da ƙarar wacce jam'iyyar APC ta shigar tana neman a dakatar da ba da kuɗaden
  • Mai shari'a Simon Amobeda ya yi fatali da ƙarar saboda abin da ya kira rashin cancantar da take da ita

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya ta zartar da hukunci kan ƙarar da jam'iyyar APC ta shigar tana neman dakatar da ba ƙananan hukumomin Kano kuɗaɗe daga asusun tarayya.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar, inda ta nemi a hana ƙananan hukumomin guda 44 samun kuɗaɗe.

Kotu ta yi hukunci a shari'ar kananan hukumomin Kano
Kotu ta yi watsi da kara kan kananan hukumomin Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta rahoto cewa kotun ta yanke hukuncin ne yayin zamanta na ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

PDP ta yi wa Shugaba Tinubu saukale, ta hango makomarsa a zaben 2027

APC ta shigar da ƙara kotu

Rahotanni sun nuna cewa shugaban jam’iyyar APC a jihar, Abdullahi Abbas, ne ya shigar da ƙarar a watan Nuwamban 2024.

APC ta kuma nemi kotu ta bayar da umarnin da zai hana gwamnatin tarayya, babban bankin Najeriya (CBN), da Akanta janar na tarayya ba da kuɗaɗe ga ƙananan hukumomin.

Waɗanda aka ambata a cikin ƙarar sun haɗa da asusun raba kuɗaɗen shiga na tarayya (FAAC), hukumar kula da rarraba kuɗaɗen shiga da tsare-tsaren kuɗi (RMAFC), ministan kuɗi da antoni janar na ƙasa.

Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, mai shari’a Simon Amobeda ya yi watsi da ƙarar, yana mai cewa ba ta cancanta ba.

Kotun ta lura cewa duk da cewa masu shigar da ƙara sun nemi janye ƙarar bayan wata kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa kotun jiha ce kawai ke da hurumin sauraron ƙarar, hakan bai samu cikar sharaɗin shigar da buƙatar janye ƙara cikin kwanaki 14 ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Taraba na shirin barin PDP zuwa ADC, hadiminsa ya tsage gaskiya

Kotu ta zartar da hukunci kan kananan hukumomin Kano
Kotu ta yi fatali da kara kan kananan hukumomin Kano Hoto: @nigerianlawyer
Source: UGC

An nemi a hukunta masu shigar da ƙara

Waɗanda ake ƙara sun nemi kotu ta yi watsi da ƙarar tare da sanya hukuncin biyan kuɗin da aka ɓata, rahoton Tribune ya tabbatar.

Lauyan antoni janar na ƙasa ya nemi a biya Naira miliyan 2.5, yayin da lauyan jihar Kano ya roƙi a biya Naira biliyan 2.

Lauyan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano Kano (KANSIEC) ya kuma nemi a biya Naira miliyan 2 bisa wahalhalun aiki, sai lauyan shugabannin ƙananan hukumomi 44 da ya nemi a biya Naira miliyan 44.

Mai shari’a Amobeda ya yanke hukuncin watsi da ƙarar gaba ɗaya ba tare da yarda a janye ta ba.

Gwamna Abba ya cika alƙawura a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana alƙawuran da ya cikawa mutanen jihar.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana cewa ya cika kaso 85% na alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya nuna cewa yana sa ran kammala cika sa ragowar a cikin shekara biyu da suka rage masa a kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng