"Ana Cin Zarafin Mata": Abin da Sanusi II Ya Gano bayan Nazarin Kotuna 9 a Kano

"Ana Cin Zarafin Mata": Abin da Sanusi II Ya Gano bayan Nazarin Kotuna 9 a Kano

  • Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce Musulmi na gari ba ya dukan matarsa, kuma masu cin zarafin ba su fahimci addini ba
  • Ya bayyana cewa malamai da limamai na da rawar gani wajen sauya halayen al’umma tare da hana fyade da dukan mata a jihar Kano
  • Sanusi ya ce yana da hujja daga Manzon Allah (SAW) cewa duk namijin da zai doki matarsa har ya ji mata rauni ba mutumin kwarai ba ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a ɗauki tsauraran matakai ga masu aikata cin zarafi na jinsi (GBV) a jihar Kano, yana mai cewa babu wani Musulmi nagari da ke dukan matarsa.

Sarki Sanusi II ya nuna matukar damuwarsa kan yadda fyade da kuma yadda maza ke dukan matansu ke zama ruwan dare a jihar.

Kara karanta wannan

Harin da Amurka ta kai Iran bai lalata cibiyoyin nukiliya ba? Trump ya yi martani

Sarki Muhammadu Sanusi ya bukaci a rika yiwa masu dukan matansu hukunci mai tsanani
Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II yayin da ya fito harabar gidan Dabo. Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Sarkin Kano ya magantu kan cin zarafin mata

Ya bayyana cewa malamai da limamai suna da muhimmiyar rawa da za su taka wajen canza ɗabi'un al'umma don kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi'a, inji rahoton Daily Trust.

Sarkin Kano ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar cibiyar DRPC da cibiyar bazarin wayar da kan Musulunci da tattaunawar addinai ta jami'ar BUK (CICID) a fadarsa da ke Kano.

Cibiyoyin sun kai ziyara fadar ne a matsayin wani ɓangare na shirin su na ba da shawarwari kan shirinsu na jagorantar shugabannin Musulmi (MOLs) don kawo ƙarshen GBV a jihohin Arewa.

Maganar Sanusi II kan dukan mata a Musulunci

A cewar Sarki Sanusi II:

"Ban taɓa yarda da dukan mata ba, kuma waɗanda suke yi, ba sa dukan matansu da niyyar gyara su. Abin da muke gani a yau duka ne na keta da cutar da mata da sunan ba su tarbiya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

"Musulunci ya girmama mata kuma ya ɗaukaka su fiye da kowane addini, kuma duk waɗanda ke neman mafaka a ƙarƙashinsa don cin zarafin mata ba su ma fahimci addinin ba.
"Duk wanda ya daki matarsa kuma ya ji mata rauni ba mutumin kirki ba ne. Ban faɗi wannan ba, Annabi Muhammad (SAW) ne ya faɗe shi. Waɗanda ba sa karatu ne kawai ba su sani ba."

Sarkin ya kuma shirin cibiyoyin ya zo a kan gaba domin yana ƙoƙarin magance ɗaya daga cikin muhimman matsalolin zamantakewa da ke shafar jihohin Arewa.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya jaddada gargadi ga masu sarauta a Kano da su guji dukan mata
Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II suna tafiya tare da fadawansa. Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Sanusi II ya jaddada maganar tsige hakimai

Ya bukaci cibiyoyin da su haɗa kai don farfaɗo da daftarin dokar iyali ta jihar Kano wadda ke magance mafi muhimman matsalolin cin zarafin mata a jihar.

Sarki Sanusi II ya ƙara da cewa:

"Dukkanin tsarin shari'a da ake buƙata suna cikin littattafanmu na shari'ar Musulunci, abin da ake buƙata shine a fitar da su kuma a haɗa su a matsayin daftari don amfani da su.
"A lokacin karatuna na PhD, wanda ke kan tsarin dokar iyali ta Musulunci, na yi nazarin kotunan Shari'a guda tara a Kano tsawon shekaru biyar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mamakon ruwan sama ya jawo ambaliya a gari, mutane 54 sun mutu

"Kuma binciken ya nuna cewa cin zarafi jinsi a zamantakewa ya zama ruwan dare a cikin al'ummarmu.
"Shi ya sa na gaya wa dukkanin hakimai da dagatai na cewa duk wanda aka kama yana dukan matarsa zai rasa rawaninsa."

"In ya mare ta, ta rama" - Sanusi II

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sarki Muhammadu Sanusi II, ya ja kunnen masu riƙe da sarautun gargajiya da su nisanci duk wani abu da zai iya sa su rasa mukamansu.

Sanusi II ya bayyana cewa duk wani basarake da aka samu da laifin dukan matarsa, ya shirya raba gari da rawaninsa, domin hakan ba abin yarda ba ne.

Ya ƙara da cewa koyaushe yana ba 'ya'yansa shawara cewa idan mijinsu ya mare su, su rama, domin babu wani uzuri da zai halatta cin zarafi a aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com