"Ba Za Mu Manta da Kai ba," An Ƙara Mutunta Buhari Kwanaki 8 bayan Allah Ya Masa Rasuwa

"Ba Za Mu Manta da Kai ba," An Ƙara Mutunta Buhari Kwanaki 8 bayan Allah Ya Masa Rasuwa

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya sauya sunan titin Shendam bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shi
  • Abdullahi Sule ya raɗawa sabon titin sunan tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari domin girmamawa da mutunta shi
  • Ya ce Buhari ya ɗauki Nasarawa a matsayin gidansa na biyu bayan Katsina, yana mai cewa daga yanzun hanyar da koma 'Titin Muhammadu Buhari'

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya canza wa sabon titin Shendam da aka kammala ginawa suna.

Gwamna Sule ya sanya wa sabon titin sunan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari domin girmamawa da mutunta shi.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
Gwamnan Nasarawa ya radawa sabon titi sunan Marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Abdullahi A. Sule
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya ƙaddamar da sabon titin mai layi biyu yayin ziyarar yini guda da ya kai jihar a ƙarshen watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya," ADC ta tona abin da gwamnatin Tinubu ta yi a rasuwar Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanya wa titi sunan Muhammadu Buhari

A halin yanzu, Gwamma Abdullahi Sule ya ce za a riƙa kiran hanyar da "Titin Muhammadu Buhari."

A taron addu’o’i na musamman da aka shirya domin tunawa da marigayin a Lafia, Gwamna Sule ya ce sauya sunan wannan titi wani mataki ne na girmamawa da ɗorewar tunawa da tsohon shugaban ƙasar.

Gwamna Sule ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta gabatar da kudirin doka a gaban majalisar dokoki domin samun goyon baya kan sauya sunan titin daga Shendam Road zuwa 'Titin Muhammadu Buhari.

Ya bayyana cewa Buhari ya ɗauki Nasarawa a matsayin gidansa na biyu bayan Katsina, don haka akwai buƙatar a mayar da wannan soyayya da girmamawa da ya nuna wa jihar, rahoton The Nation.

Gwamna Sule ya jinjinawa Shugaba Tinubu

Gwamnan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa girmamawar da ya nuna wa tsohon shugaban bayan rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Malami ya shawarci iyalan Buhari, ya ce yan Najeriya na da hakki a dukiyarsu

“Ina ƙara gode wa Shugaba Ahmed Bola Tinubu bisa girmamawa da mutunta wa da ya bai wa marigayin Shugaba Buhari. Babu wani shugaban ƙasa da aka mutunta haka a lokacin birne shi kamar Muhammadu Buhari.
"Mun gode da yadda Shugaban Tinubu ya tura mataimakin shugaban ƙasa zuwa London domin ɗauko gawar, sannan kuma ya je a Katsina domin karɓarta da kansa."

- Gwamna Abdullahi Sule.

Gwamna Sule da Muhammadu Buhari.
Gwamna Sule ya yabawa Shugaba Tinubu bisa yadda ya girmama Buhari Hoto: Abdullahi A. Sule
Source: Facebook

Abdullahi Adamu ya yabawa Gwamna Sule

A nasa jawabin, tsohon gwamnan Nasarawa kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yabawa Gwamna Sule kan wannan yunkuri na tunawa da marigayin.

“Ina da tabbacin cewa ba ƴaƴansa kaɗai za su ji daɗin wannan taron addu'a ba, har ma da mu da muka ƙaunace shi, muka yi rayuwa a ƙarƙashinsa lokacin da yake shugaban ƙasa, mun ji daɗin hakan.
"Muna kuma godiya da ƙoƙarin Mai Girma Gwamna da kuma ubanmu, Sarkin Lafia, bisa ɗaukar nauyin wannan zaman addu’a don tunawa da Muhammadu Buhari,” in ji shi.

An yi wa Buhari addu'o'i a cocin ƙasa

A wani rahoton, kun ji cewa mabiya addinin kirista sun gudanar da taron addu'o'in nema wa Buhari rahama a babbar coci ta ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Kamar ya sani," Kalaman da Buhari ya faɗa game da mutuwarsa kafin ya sauka daga mulki

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ce ta shirya domin karrama marigayi tsohon shugaban ƙasa.

Rahoto ya nuna cewa taron addu'ar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ministoci, ‘yan majalisa da tsofaffin jami’ai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262