ABUAD: Asibitin Najeriya da Aka Yi Hasashen Buhari Zai Rayu da Ya Yi Jinya a can
- Dr. Akinola Akinmade ya ce asibitin ABUAD da ke Ado-Ekiti na da kayan aiki da ƙwararrun likitoci da za su iya ceto Muhammadu Buhari
- A cewar shugaban asibitin, da yanzu tsohon shugaban kasar yana rayuwarsa kuma yana murmurewa da a asibitin ya yi jinyarsa
- Ya bukaci gwamnati ta hana dogaro da jinya a ƙasashen waje ta hanyar zuba jari a manyan cibiyoyin lafiya na gida kamar asibitin ABUAD
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti – Shugaban asibitin jami'ar Afe Babalola (ABUAD), Dr. Akinola Akinmade, ya ce asibitin na da kayan aiki da likitocin da za su iya ceto rayuwar Muhammadu Buhari.
A cewar Dr. Akinola, da asibitin ABUAD da ke Ado-Ekiti ne Buhari ya yi jinya, to da ba shakka yanzu yana nan yana rayuwa kuma yana murmurewa daga rashin lafiyarsa.

Source: Twitter
Likita ya so Buhari ya yi jinya a asibitinsu
Shugaban asibitin ya nanata irin ƙwararrun likitocin da ke asibitin, da kayan aikin da suke da shi, wanda ya ce za su iya ceto rayuwar Buhari, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da yake magana da manema labarai a karshen mako a Ado-Ekiti, shugaban asibitin ya koka kan yadda ake ta yawan fita kasashen waje domin neman magani.
Ya yi nuni da cewa shugabannin siyasa da kuma masu hannu da shuni a Najeriya sun dauki dabi'ar kyale asibitocin kasar zuwa kasashen waje yin jinya.
Dr. Akinola ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta zuba jari a cikin cibiyoyin lafiya na gida, inda ya ce asibitin ABUAD ya zama abin koyi a fadin kasar.
Kwarewar likitoci da kayan aiki a ABUAD
A cewarsa, asibitin ABUAD ya kasance shi ne mafi inganci a yankin Afrika ta Kudu da ma kasashen Sahara, kana yana da manyan likitoci da kayan aiki na zamani.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Rikakken dillalin kwayoyi ya shiga hannu bayan shekara 6 ana nemansa
A cewarsa, babu wani asibitin jami'a a Najeriya ko ma a Afrika da ke da kayan aiki da na’urorin zamani da yawan likitoci da masana daga ƙetare kamar yadda asibitinsu ke da su.
Ya ce duk wadannan ci gaba sun faru ne sakamakon hangen nesa da kishin kasa na wanda ya kafa asibitin, babban lauya kuma jigo a fannin shari’a, Afe Babalola (SAN).

Source: Facebook
An ba 'yan Najeriya shawara kan kiwon lafiya
Dr. Akinola ya ce an kafa asibitin ne da nufin ganin cewa kowanne dan kasa, mai hali ko mara hali, na iya samun kiwon lafiya mai inganci ba tare da fita kasar waje ba.
Jaridar New Telegraph ta rahoto shugaban asibitin ya ƙara da cewa:
“A bara ne, asibitinmu, karkashin jagorancin Afe Babalola (SAN), ya kulla haɗaka da Marengo Asia Hospitals, wani babban rukuni na asibitoci da ke India.
“Bayan fara wannan haɗin gwiwa, likitocin Marengo daga India tare da hadin gwiwar likitocinmu na Najeriya sun gudanar da tiyatar dasa koda guda tara a AMSH."
A ƙarshe, Dr. Akinmade ya jaddada cewa Najeriya ba za ta kuɓuta daga tsarin mulkin mallaka ba har sai ta inganta kiwon lafiyarta, ta yadda ba za a ƙara dogara da zuwa kasashen waje domin neman lafiya ba.

Kara karanta wannan
London Clinic: An gano makudan kudi da ake biya kullum a asibitin da Buhari ya rasu
Asibitin da Buhari ya yi jinya a London
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a asibitin London Clinic bayan ya kwashe tsawon kwanaki 230 yana karɓar magani.
Wannan asibitin da ke tsakiyar birnin Landan na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin lafiya da ke karɓar shugabanni, sarakuna da fitattun ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na duniya.
London Clinic yana da dogon tarihi wajen jinyar masu mulki da manyan masu hannu da shuni, sai dai akwai zarge-zargen da ake yi wa cibiyar, misali, fitar da bayanan marasa lafiya.
Asali: Legit.ng
