Bayanai Sun Ci Karo da Juna kan Nadin da Tinubu Ya Yi wa Ɗan IBB

Bayanai Sun Ci Karo da Juna kan Nadin da Tinubu Ya Yi wa Ɗan IBB

  • Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Muhammed Babangida ya karɓi naɗin shugaban Bankin Noma da Bola Tinubu ya yi masa
  • Wannan ya ci karo da sanarwar da ke yawo a baya cewa ɗan tsohon shugaban ƙasa, Muhammed Babangida ya yi watsi da muƙamin
  • Sanarwar da hadimin Shugaban kasa, Dada Olusegun ya fitar, ta ce labarin baya ƙagagge ne kuma za a ɗauki mataki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata cewa Muhammed Babangida, ɗan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya yi watsi naɗin Bola Tinubu.

Sanarwar da ya fitar ta ce Muhammed Babangida, ya amince da nadin da aka yi masa a matsayin shugaban rikon ƙwarya na Bankin Noma na Ƙasa (BOA).

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya," ADC ta tona abin da gwamnatin Tinubu ta yi a rasuwar Buhari

Bola Tinubu fa Muhammadu Babangida
Dan IBB ya amshi muƙamin Tinubu Hoto: @aonanuga1956/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mai taimaka wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin kafofin sada zumunta, Dada Olusegun ya bayyana haka a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin ɗan IBB ya ƙi muƙamin Tinubu

A wata wasiƙa da ta karaɗe shafukan sada zumunta, ta ce Muhammed Babangida ya yi watsi da muƙamin, amma daga baya aka yi zargin labarin ƙarya ne.

Amma a saƙon gaggawa da Fadar Shugaban ƙasa ta fitar, ta ce Muhammed Babangida ya nuna godiya bisa amincewar da shugaban ƙasa ya yi na naɗinsa.

Sanarwar ta ce:

"A cikin wata sanarwa da Babangida ya fitar, ya bayyana cewa rahotannin da ke cewa ya ƙi karɓar mukamin ba gaskiya ba ne, kuma an ƙirƙiro su ne da mugun nufi."
"Ya bayyana irin waɗannan ikirari a matsayin yunkuri na yaudara da ƙoƙarin ɓata sunan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu."

Sanarwar ta jaddada cewa ba Muhammed Babangida ne ya fitar da sanarwar ba, kuma yana tare da gwamnati.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ɗauko ɗan IBB da wasu ƴan Arewa 7, ya ba su manyan muƙaman gwamnati

Gwamnatin Tinubu ya shawarci jama'a

Fadar shugaban ƙasa ta shawarci jama'a da su yi watsi da takardar da ke yawo kan cewa Muhammed Babangida ya yi watsi da muƙamin da aka ba shi.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Fadar shugaban kasa ta karyata cewa ɗan IBB ya ƙi muƙaminta Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanarwar ta ce"

"Muna so mu bayyana cewa Muhammed Babangida ya amince da nadin da gwamnatin tarayya ta sanar da shi a matsayin shugaban Bankin Noma, tare da nuna godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da kwarewarsa."

Sanarwar ta ƙara da cewa ana ci gaba da gano waɗanda ke yaɗa wannan ƙarya, kuma za a hukunta su yadda doka ta tanada.

"Muna kuma tabbatar wa al’umma cewa za a gudanar da bincike kan waɗanda ke yaɗa waɗannan ƙagaggun labarai, kuma za a ɗauki matakin da ya dace a kansu."
"Gwamnatin nan na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, adalci da haɗin kai a tsakanin 'yan ƙasa."

Tinubu ya naɗa ɗan IBB muƙami

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Muhammad Babangida a matsayin shugaban sabuwar hukumar Bankin Noma (BoA).

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya fara fuskantar matsala a ADC kwanaki kaɗan bayan ya fice daga PDP

Wannan naɗi ya kasance cikin wani muhimmin mataki da shugaban ƙasa ya ɗauka domin ƙarfafa bangaren noma da farfaɗo da muhimman hukumomin gwamnati.

Sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar ta cehugaban ƙasa ya kuma amince da naɗin wasu mutane takwas, inda aka tura su hukumomi daban-daban na gwamnatin tarayya a

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng