Dangin Buhari Sun Lissafa Mutum 34 Sun Musu Godiya bayan Gama Zaman Makoki
- Malam Mamman Daura ya gode wa Shugaba Bola Tinubu da matarsa bisa taimako kan rashin lafiya da rasuwar Muhammadu Buhari
- Dangin Buhari sun nuna godiya ga kasashen duniya, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da suka jajanta musu
- Iyalan sun ce irin addu’o’i da goyon bayan da suka samu sun kara musu kwarin gwiwa wajen jure babban rashin da suka yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Mafi shekaru a dangin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Mamman Daura, ya yi godiya ga jama'a bayan gama zaman makoki.
Ya yi godiya ga ‘yan Najeriya da sauran mutane daga kasashe daban-daban da suka jajanta musu bayan rasuwar Buhari.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Mamman Daura ya yi ne a cikin wano sako da aka wallafa a shafin tsohon shugaban kasar na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Godiya ga shugaban kasa da gwamnati
Malam Mamman Daura ya bayyana cewa dangin sun samu goyon baya daga shugaba Bola Ahmed Tinubu da uwargidansa, Sanata Remi Tinubu.
Haka zalika ya ce sun samu goyon bayan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya kai musu ziyara a Burtaniya da kuma Daura.
Malam Mamman Daura ya ce:
“Mun gode ƙwarai ga shugaban kasa bisa hukuncin da ya yanke na ayyana hutu da kuma yadda aka sake wa Jami’ar Maiduguri suna.
"Wannan gagarumin alheri ne da ya kara mana kwarin gwiwa.”
Haka zalika, ya nuna jin dadin yadda ministoci da sauran jami’an gwamnati suka nuna musu kulawa.
Godiya ga kasashen duniya da sarakuna
Dangin Buhari sun nuna godiya ga masu fada a ji daga sassan duniya kamar Sarki Charles III na Ingila.
Sun yi godiya ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da mataimakiyarsa Amina Mohammed, shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, da sauran shugabannin ECOWAS.
Iyalan sun yi godiya ga sarakunan gargajiya da suka hada da Sultan na Sokoto, Shehun Borno, Sarkin Gwandu, da kuma manyan sarakunan Katsina da Daura.
Godiya ga Atiku, Dangote da sauransu
A cewar sanarwar, dangin sun gode wa tsofaffin mataimakan shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Farfesa Yemi Osinbajo.
Haka zalika sun godewa Babagana Kingibe, da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da sauran shugabannin majalisa.
Sun kuma nuna godiya ga manyan ‘yan kasuwa irin su Aliko Dangote, Abdul Samad Rabi’u, Muhammadu Indimi, Dahiru Mangal, Kola Adesina da Nasiru Danu.

Source: Twitter
Godiya ga jama’a baki daya
Yayin gode wa dukkan jama'ar da suka taya su alhini, Malam Mamman Daura ya ce:
“Mutane sun fito kwansu da kwarkwata wajen halartar jana’iza da addu’a ga Buhari. Muna matukar godiya da fatan Allah ya saka musu da alheri.”
Ya ce dangin suna jinjinawa jama’a daga dukkan matakai – gwamnati, jami’an tsaro, kungiyoyin al’umma, da kafafen yada labarai – bisa yadda suka nuna soyayya da mutuntawa ga marigayin.
Malam Mamman Daura ya yi godiya ga malaman addinin Musulunci da na Kirista da suka taya su alhini.

Kara karanta wannan
An gano bidiyon Aisha Buhari tana rusa kuka a gaban Shettima yayin da ya ke ta'aziyya
Jerin sunayen mutane 34 da dangin Buhari suka ambata:
1. Shugaba Bola Ahmed Tinubu
2. Uwargidansa, Sanata Remi Tinubu
3. Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima
4. Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda
5. Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum
6. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar
7. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo
8. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo
9. Babagana Kingibe
10. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
11. Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajuddeen Abbas
12. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin
13. Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume
14. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha
15. Shugaban Ma’aikata na yanzu, Hon. Femi Gbajabiamila
16. Tsohon Shugaban Ma’aikata, Farfesa Ibrahim Gambari
17. Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi
18. Sarkin Musulmi, Sultan na Sokoto
19. Shehun Borno
20. Sarkin Gwandu
21. Sarkin Katsina
22. Sarkin Daura
23. Alhaji Aliko Dangote
24. Abdul Samad Isyaka Rabi’u
25. Alhaji Muhammadu Indimi
26. Alhaji Dahiru Mangal
27. Kola Adesina
28. Nasiru Danu
29. Sarkin Ingila, Sarki Charles III
30. Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
31. Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed
32. Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka (AU)
33. Shugaban Kwamitin Shugabannin Kasashen ECOWAS
34. Tsohon Shugaban Kasa, Janar Abdulsalami Abubakar
An yi wa Buhari takwara a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa wani matashi a jihar Bauchi, Malam Danladi Mai Kaset ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari takwara.
Danladi Mai Kaset ya ce ya sanya wa dan shi suna Muhammadu Buhari ne saboda kyawawan halayen tsohon shugaban kasar.
Sheikh Isa Ali Pantami da ya yi aiki tare da shugana Buhari, ya ba matashin kyautar N200,000 domin sayen rago da hidimar suna.
Asali: Legit.ng


