'Ya Yi Mani Albishir Zan Yi Tazarce,' Tinubu Ya Fadi Wanda Ya Taimaka Ya Zama Shugaban Kasa

'Ya Yi Mani Albishir Zan Yi Tazarce,' Tinubu Ya Fadi Wanda Ya Taimaka Ya Zama Shugaban Kasa

  • Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa marigayi Sikiru Kayode Adetona, tsohon sarkin Ijebuland, ya yi masa addu’a kan zaben 2027
  • Ya bayyana cewa Sarkin, wanda ya rasu yana da shekaru 91 a duniya ya ba shi tabbacin zai yi nasara a karo na biyu idan ya tsaya takara
  • Tinubu ya tuna irin goyon bayan da marigayi sarkin ya bayar a lokacin gwagwarmayarsu, yana mai bayyana shi a matsayin jagora na gari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa marigayi Sikiru Kayode Adetona, tsohon sarkin Ijebuland, ya shaida masa cewa zai samu nasara a zaben 2027.

Adetona ya rasu ne a ranar Lahadi da ta gabata yana da shekaru 91 a duniya, kuma an yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.

Kara karanta wannan

Awujale: Yadda basarake ya assasa kafa APC, nasarar Buhari a 2015

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Tinubu ya yi jimamain rasuwar Sarkin Ijebulanda, Sikiru Kayode Adetona Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa mutuwarsa ta biyo bayan sanarwar rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda shi ma abokinsa ne na dogon lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya halarci addu’ar marigayi sarkin Ijebu

The Nation ta ruwaito an gudanar da addu’ar fidau ta kwana takwas domin marigayi sarki a filin wasa na Dipo Dina International Stadium, da ke Ijebu Ode, Jihar Ogun, a ranar Lahadi.

Shugaba Tinubu, wanda ya halarci wannan taro, ya danganta nasararsa a zaben 2023 da albarka da kuma addu’ar da ya samu daga Awujale.

Ya ce:

"Ina gode wa Allah madaukakin Sarki da ya bani damar tsayawa a gabanku a matsayin shugaban ƙasar Najeriya."
"Nasarata ta samo asali ne daga goyon bayanku da kuma addu’ar marigayi Awujale."

Addu’ar tsohon sarki ga Tinubu

Shugaban ƙasar, wanda tuni ake hasashen zai tsaya takarar wa’adi na biyu, ya ce marigayi sarkin ya yi masa addu’a tare da shaida masa cewa tabbas zai yi nasara.

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

A cewarsa:

"Na je wajensa, ya yi min addu’a, ya ce, za ka ci karo na biyu (na mulkin Najeriya)."

Tinubu ya ci gaba da cewa:

"Yau ya tafi. Ya bar mu.”

Ya kuma gode wa gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa irin kulawar da ya bai wa marigayi sarkin har zuwa lokacin rasuwarsa, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai gaskiya da kima.

Marigayi Sarkin Ijebuland
Tinubu ya ce marigayi Sarkin Ijebu ya masa albishir da nasara a 2027 Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Shugaban ƙasar ya ce:

"Baba kullum yana tare da mu a lokacin da muke cikin buƙata. Ina iya tuna lokacin ranar 12 ga watan Yuni, zanga-zangar da muka yi, ziyarar da muka kai fadarsa, adawarmu da soke zabe, da ƙudurimu na ganin an dawo da sahihancin zaben."

An gano basaraken da ya taimaki APC

A wani labarin, kun ji cewa Fasto Tunde Bakare, babban mai kula da Cocin Global Community Citadel, ya bayyana godiya ga Shugaba, Bola Tinubu bisa shirya jana'izar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa

Haka kuma , Fasto Bakare ya miƙa gagarumar jinjina ga marigayi Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona, wanda shi ma ya rasu a rana ɗaya da Buhari da su ke abokan juna.

A cewar Fasto Bakare, marigayi Awujale, duk da cewa ba ɗan siyasa ba ne, ya taka babbar rawa wajen kafa jam’iyyar APC, wacce daga baya ta kai ga nasarar Muhammadu Buhari a zaɓen 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng