Yadda Kiristoci Suka Yi wa Buhari Addu'a a Babban Cocin Kasa na Abuja

Yadda Kiristoci Suka Yi wa Buhari Addu'a a Babban Cocin Kasa na Abuja

  • Gwamnatin tarayya ta shirya babban taron coci na alhinin mutuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana Buhari a matsayin jajirtaccen shugaba mai gaskiya
  • Rahoto ya nuna cewa taron addu'ar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ministoci, ‘yan majalisa da tsofaffin jami’ai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta gudanar da addu'a a coci domin tunawa da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 20 ga Yuli, 2025.

Wannan biki na daga cikin jerin abubuwan girmamawa da gwamnati ta gudanar don girmama tsohon shugaban.

Kiristoci yayin da suka yi wa Buhari addu'a a coci
Kiristoci yayin da suka yi wa Buhari addu'a a cocin Abuja. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Tsohon hadimin shugaba Buhari a fannin yada labarai, Bashir Ahmad ya wallafa hotunan yadda aka yi addu'ar a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron addu'ar ya samu halartar manyan baki da dama daga gwamnatin tarayya da sauran bangarorin gwamnati.

Kara karanta wannan

An fara fito da bayanai kan 'cabal', Gambari ya fallasa yadda aka mamaye gwamnatin Buhari

Ana fatan wannan biki zai karfafa wa ‘yan Najeriya gwiwa wajen yin nazari kan rayuwa da jagorancin Buhari.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ce Buhari ya kasance shugaba mai nagarta wanda ya yi aiki da gaskiya da kishin kasa, kuma ya bar tarihi mai kyau.

Akume ya yaba wa shugaba Buhari

A yayin jawabinsa, Sanata Akume ya bayyana marigayi Muhammadu Buhari a matsayin shugaba wanda ya jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da gyaran hukumomi a Najeriya.

The Nation ta wallafa cewa Akume ya ce ba za a ce Buhari ba shi da kuskure ba, amma ya yi abin da za a cigaba da tuna wa da shi.

Ya ce:

“Duk da cewa dan Adam ajizi ne, ya yi kokari sosai kuma ya bar tarihi mai kyau. Tarihin da ya bari cikin sha’anin tsaro, kariyar al’umma da masana’antar mai ya kasance abin tunawa da shi a Najeriya.”

Girmamawar da Tinubu ya yi wa Buhari

A wani bangare na bikin, Sanata Akume ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari, a matsayin girmamawa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Za a yi wa shugaba Buhari addu'a a coci ranar Lahadi

Ya bayyana hakan da cewa:

“Hakan yana da nufin zaburar da matasa su yi shugabanci da sadaukarwa kamar yadda Buhari ya yi.”

Wannan mataki ya kasance wani bangare na nuna godiya da karramawa ga rawar da Buhari ya taka a ci gaban Najeriya.

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

Mutanen da suka halarci taron cocin

An yi taron ne a babban cocin kasa da ke Abuja, inda wakilan shugaban majalisar dattawa, ‘yan majalisar tarayya, ministoci da tsofaffin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya suka halarta.

Biki ne da ya kawo karshen bukukuwan mako guda na tunawa da marigayi Buhari, wanda ya mutu a birnin London kuma aka birne shi a Daura, jihar Katsina.

Kwankwaso ya je ta'aziyya gidan Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara gidan marigayi shugaba Muhammadu Buhari.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ziyarar ne domin yin ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban kasar da ya rasu.

Kafin zuwa gidan tsohon shugaban, Kwankwaso ya tsaya a fadar mai martaba sarkin Daura domin masa ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng