Gwamna Dikko Radda Ya Yi Bayani daga Asibiti bayan Haɗarin Mota

Gwamna Dikko Radda Ya Yi Bayani daga Asibiti bayan Haɗarin Mota

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda ya samu damar yin bayani daga gadon asibitin da ake duba lafiyarsa
  • Gwamnan da wasu da ya ke tafiya da su zuwa Daura daga Katsina sun gamu da iftila'in haɗarin mota da ya jikkata jama'a
  • A gajeren bayanin da ya yi, gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa suna samun sauƙi sosai yayin da ake ci gaba da duba su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, ya bayyana cewa yana samun sauki bayan da ya gamu da haɗarin mota a hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa haɗarin ya rutsa da gwamnan ne a hanyarsa ta kai ziyara garin Daura, mahaifar tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya yi hatsari, an ji halin da yake ciki

Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda
Gwamna Dikko Radda ya yi magana daga asibiti Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Twitter

A wani bidiyo da Maiwada Dammallam, ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga gwamman asibiti, inda ya ce jiki yana yin kyau sosai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Dikko: "Allah Ya jarrabce mu da haɗarin mota"

A cikin faifan bidiyon da Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a shafin Facebook, ana iya jin karar na’urorin asibiti yayin da gwamna Dikko Radda ke bayani cikin natsuwa.

Ya ce:

"Allah Ya jarrabce mu da haɗarin mota, amma mun samu sauƙi Alhamdulillah."
"Muna nan, ana ci gaba da duba mu domin samun cikakken sauki. Al’umma muna godiya da addu’o’in da ake ta mana."

Gwamnan, wanda ake iya ganin alamun yana jin ba daɗi a fuskarsa ya jaddada godiya ga dukkanin wadanda ke yi masu fatan alheri.

Gwamnan jihar Katsina ya yi haɗarin mota
Dikko Radda ya ce yana samun sauƙi Hoto: Dr. Umaru Dikko Radda
Source: Facebook

Ya kara da bayar da tabbacin cewa sauƙi yana samuwa sosai, yayin da likitoci ke ci gaba da aikin duba ladiyarsu.

Dikko Radda: Al’umma na ci gaba da addu’a

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, an kai Ganduje jinya a asibitin London? Hadiminsa ya magantu

Daga cikin masu kallon bidiyon da suka tofa albarkacin bakinsu, da dama sun bayyana fatan alheri ga gwamnan da sauran mutanen da haɗarin ya rutsa da su.

Ahmed Hassan Mashi ya ce:

“Masha Allah! Alhamdulillah!! Allah SWT Ya ba ku lafiya kuma Ya ƙara tsare gaba.”

Ibrahim Ahmed ya rubuta:

“Alhamdulillah, godiya ga Allah. Da fatan Allah Ya ƙara tsare ku da kariyarSa, kuma Ya ba ku lafiya, amin.”

Bala Nuhu ya ce:

“Masha Allah, Alhamdulillah. Allah ya ƙara tsare ka, ya kuma hana aukuwar irin haka nan gaba.”

Mafita M. Bello ta ce:

“Allah ya ba ka lafiya, ya tsare gaba. Ubangiji Allah ya kare ka da duk abin da kake yi, Ameen ya Hayyu ya Ƙayyum.”

Gwamnan Dikko Radda ya yi haɗari

A wani labarin, kun ji cewa rahotanni daga jihar Katsina sun tabbatar da cewa gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, ya gamu da haɗarin mota a ranar Lahadi.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta jaddada cewa hatsarin ba mai tsanani ba ne, kuma gwamnan yana cikin ƙoshin lafiya yayin da ake duba lafiyarsa.

Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan afkuwar haɗarin a hanyar zuwa Daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng