Bayan Buhari, an Kai Ganduje Jinya a Asibitin London? Hadiminsa Ya Magantu

Bayan Buhari, an Kai Ganduje Jinya a Asibitin London? Hadiminsa Ya Magantu

  • A yau Lahadi 20 ga Yuli 2025, rahotanni sun yaɗu cewa an kwantar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje a asibiti a London
  • Sai dai Salihu Tanko Yakasai ya musanta rahoton, yana mai cewa Ganduje na cikin koshin lafiya kuma bai kwanta a asibiti ba
  • Yakasai ya bayyana cewa Ganduje ya tafi London kafin rasuwar Muhammadu Buhari da kafarsa, kuma ba don jinya ya tafi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - A yau Lahadi 20 ga watan Yulin 2025 aka yi ta yada cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje bai da lafiya.

Rahotannin suka ce wai an kwantar da Ganduje a wani asibiti da ke birnin London a kasar Birtaniya.

An ƙaryata labarin kwantar da Ganduje a asibitin London
An samu bayanai kan rade-radin cewa an kwantar da Ganduje a asibitin London. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

Karin bayani kan rade-radin rashin lafiyar Ganduje

Sai dai wani makusancinsa, Salihu Tanko Yakasai ya tsage gaskiya yayin hira da DCL Hausa da aka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

London Clinic: An gano makudan kudi da ake biya kullum a asibitin da Buhari ya rasu

Yakasai ya yi fatali da rahoton da ake yaɗawa inda ya ce lafiyarsa kalau babu abin da yake damun tsohon gwamnan Kano.

A cewarsa:

"Wannan labari da yake zagawa na rashin lafiyar mai girma tsohon shugaban APC, kuma shugaban hukumar FAAN, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba gaskiya ba ne.
"Lafiyarsa kalau ba wani kwanciya a asibiti, babu wani abin da ke damunsa yana cikin koshin lafiya."
Abin da muka sani kan rade-radin rashin lafiyar Ganduje
Na kusa da Ganduje cewa mai gidansa na asibitin London. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

'Babu abin da ke damun Ganduje' - Yakasai

Makusancin Gandujen ya tabbatar da cewa tabbas mai gidan nasa yana London kuma da ƙafarsa ya je lafiya lau babu abin da ke damunsa.

Ya bayyana cewa ya je kasar ne domin gudanar da wasu abubuwa masu muhimmanci ba wai rashin lafiya ba ne ya kai shi.

Yakasai ya ce yana da tabbacin da zarar mai girma Ganduje ya kammala abubuwan da suka kai shi zai dawo gida idan Allah ya yarda.

Ya ce:

Kara karanta wannan

An gano dalilin Ganduje na rashin tarbar Tinubu a Kano

"Kuma kwarai da gaske yana London amma da kafarsa ya tafi, ya tafi kafin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
"Ya tafi da niyyar yin waɗansu abubuwa amma dai ba rashin lafiya ba ne ya kai shi."
"Gaskiya babu gaskiyar wannan magana kuma yana nan idan ya gama abubuwan da suka kai shi zai dawo gida in shaa Allahu."

Da aka tambaye shi kenan babu wata maganar jinya da ke cewa Ganduje na yi a London? Sai Yakasai ya ce:

"Kwarai babu wata maganar jinya lafiyarsa lau, ina mai tabbatar maka da wannan."

Yakasai ya ce yana zaton Ganduje ya je London kwana biyu kafin rasuwar Buhari inda ya ce yana tsammanin ya yi musu ta'aziyya sai dai ba a yi bidiyo ko hoto ba.

Buhari: Kudin da ake kashewa a asibitin London

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a asibitin London bayan ya kwanta rashin lafiya duk da cewa an shirya sallamarsa a ranar.

Asibitin da Buhari ya mutu ya na cikin mafi tsada a Burtaniya, inda ake biyan har £3,500 (N7m) kullum a dakin ICU domin marasa lafiya.

Dan uwansa, Mamman Daura ya ce Buhari yana cikin koshin lafiya ranar Asabar kafin ya fuskanci matsananciyar numfashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.