Gwamna Bago Ya Gayyato Mutanen China, Za Su Fantsama cikin Harkar Noma a Neja

Gwamna Bago Ya Gayyato Mutanen China, Za Su Fantsama cikin Harkar Noma a Neja

  • Gwamnatin Neja ta jagoranci masu zuba jari daga China zuwa Rabba domin duba wuraren da za a kafa masana’antun sarrafa noma
  • Kwamishinan kasuwanci ya bayyana cewa shirin zai samar da wuta mai dorewa, ayyukan yi, hanyoyi da kuma bunkasa tattalin arziki
  • Masu zuba jari daga China sun yi alkawarin fara aiki da zarar an kammala cike ka'idoji, yayin da Sarkin Rabba ya ba su goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - A wani bangare na shirin 'Sabuwar Neja' gwamnatin Neja ta jagoranci wasu masu zuba jari daga kasar China zuwa Rabba, karamar hukumar Mokwa.

Gwamna Mohammed Umaru Bago, ta hannun kwamishinan kasuwanci da zuba jari, Alhaji Aminu Takuma, ne ya jagoranci 'yan Chinan, inda suka duba wurin da za a kafa masana’antu na sarrafa amfanin gona.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

Gwamnatin Neja ta gayyato 'yan China don su gina masana'antun noma
'Yan China sun karbi gayyatar gwamnatin Neja, sun duba wuraren gina masana'antun noma. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Gwamnatin Neja ta gayyato 'yan China

Ziyarar, wadda ta gudana a ranar 16 ga Yuli, 2025, ta fara ne da kai ziyara ta girmamawa ga Ndashin (Sarkin) Rabba, Injiniya Alhaji Umaru Tswako, a cewar rahoton NTA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa Alhaji Aminu Takuma ya nemi goyon bayan al’ummar yankin Rabba domin aiwatar da wannan ci gaban da ake kokarin kawo wa.

Alhaji Takuma ya jaddada cewa Gwamna Umaru Bago na da cikakkiyar niyya ta ganin Rabba ta shiga sahun wuraren da za su fi amfana da wannan shiri.

Tawagar ta hada da Mr. Yomi, Shugaban Special Agro-Processing Zone (SAPZ) na jihar Neja, da kuma Hon. Zakariyau Rabba, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

'Yan China sun duba wurin sarrafa noma

Da yake jawabi ga dattawa da shugabannin gargajiya, Alhaji Takuma ya bayyana irin amfanin da aikin zai haifar, ciki har da samuwar wutar lantarki mai ɗorewa, gyaran hanyoyi, samar da ayyukan yi da kuma habakar tattalin arzikin yankin Rabba.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari, Bola Tinubu zai je jihar Kano ta'aziyyar Aminu Dantata

A martaninsa, Sarkin Rabba ya nuna cikakken goyon bayan al’umma tare da nada wakilai da za su raka tawagar duba wuraren aikin.

Tawagar ta zagaya filayen noma, bakin Kogin Neja, da kuma tsofaffin wuraren da kamfanin Sunflag Agro Nigeria Limited ke amfani da su.

Masu zuba jari daga kasar Sin sun nuna gamsuwa da wuraren da aka ziyarta da kuma albarkatun da ake da su, tare da bayyana shirin fara aiki da zarar an kammala dukkanin izini da matakan da suka dace.

'Yan China za su kulla kasuwanci da Neja

Ko a ranar 22 ga Fabrairu, 2025, wata tawaga daga kasar China ta nuna sha’awar yin hadin gwiwa da gwamnatin Neja don inganta sashen noma da hakar ma’adinai.

Shugaban tawagar ya bayyana hakan ne lokacin da Gwamna Bago ya kai ziyarar girmamawa ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Mohammed Namadi Sambo, a ofishinsa da ke Abuja.

Shugaban ‘yan kasuwar ya bayyana cewa sun zabi Neja domin fara wannan hadin gwiwa ne saboda tana gaba a fannin ci gaban noma da yawan albarkatun kasa idan aka kwatanta da sauran jihohi.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

Ya ce hadin gwiwar za ta kasance bisa tsarin daidaito a bangaren kudi, kayan aiki da kuma ƙwarewa domin cimma nasara, a cewar sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin Neja.

'Yan China sun duba wuraren da za su kafa masana'antun noma a jihar Neja
Tawagar 'yan China da suka je garin Rabba da ke jihar Neja don kafa masana'antun noma. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Gwamnan Neja ya ba 'yan China hadin kai

A bayaninsa, Gwamna Bago ya nuna farin cikinsa da shirin, tare da tabbatarwa da masu zuba jari cewa jihar Neja za ta samar da yanayin kasuwanci mai kyau da sauki.

Ya bayyana cewa jihar tana da babbar damar bunkasa fannin noma da ma’adinai, wanda har yanzu ba a ciro cikakken amfani daga gare su ba.

Haka kuma, an gabatar wa da gwamna wani shirin ci gaban noma na zamani wanda ya kunshi noman hatsi, kiwo, da tsarin yadda aka sarrafa amfanin gona da aka aiwatar a fili mai fadin hekta 2,000 a kasar Turkiyya.

An kama 'yan China suna rayuwa a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro a Najeriya sun kama wasu ‘yan kasar China da suka shigo ƙasar suka zauna ba tare da samun sahihiyar takardar izinin zama ba.

An cafke su ne a wajen aikin samar da wutar lantarki da ake gudanarwa a wani yanki na jihar Neja da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Rahotannin da muka tattara sun nuna yadda aka gano su tare da bayanin yadda suka dade suna zama a ƙasar ba tare da wata matsala ko bincike ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com