"Sun Yi Yawa": Gwamnatin Borno Fadi Dalilin Kasa Biyan Mafi Karancin Albashin N70,000

"Sun Yi Yawa": Gwamnatin Borno Fadi Dalilin Kasa Biyan Mafi Karancin Albashin N70,000

  • Gwamnatin jihar Borno ta fito ta wanke kanta kan dalilin kasa biyan ma'aikatan ƙananan hukumomi mafi ƙarancin albashi
  • Ta bayyana cewa ma'aikatan ƙananan hukumomi sun yi yawan da ba zai yi wa a riƙa biyansu mafi ƙarancin albashin ba
  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomi da su koma yankunansu don samun mafita kan batun

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnatin Borno ta bayyana dalilan da yasa ba zai yiwu a aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar ba.

Gwamnatin ta bayyana dalilinta ne a wata ganawa ta musamman da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Maiduguri a daren ranar Asabar.

Gwamnatin Borno ta yi magana kan biyan mafi karancin albashi
Gwamnatin Borno ta ce ba za ta iya biyan mafi karancin albashin N70,000 ba Hoto: @ProfZulum
Source: Facebook

The Punch ta ce babban sakataren ma’aikatar harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Modu Alhaji Mustapha, ya bayyana cewa kasa aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙananan hukumomi na da nasaba da yawan ma’aikata.

Kara karanta wannan

Duk da suna cikin hadaka, El Rufai da Peter Obi sun ki komawa ADC, an ji dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka kasa biyan sabon albashin?

A cewarsa, ƙananan hukumomin jihar Borno na fama da yawan ma’aikata, wanda hakan ke haifar da tangarda wajen biyan albashi da gudanar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.

Ya bayyana cewa ƙananan hukumomi 27 da ke jihar suna da ma’aikata kimanin 90,000, wanda hakan adadi ne mai yawa fiye da wanda ake da shi a wasu jihohi masu yawan jama’a.

Ya ce kamar jihar Kano wadda ke da yawan mutane sun ninka na Borno sau uku tana da ma’aikata kimanin 30,000 kacal a cikin ƙananan hukumomi 44.

“Ko da yake burin aiwatar da mafi ƙarancin albashi abu ne mai kyau, gaskiyar da muke fuskanta a jihar Borno abin na da matuƙar wahala."
"Ƙananan hukumominmu sun cika da ma’aikata, kuma yawan ma’aikatan da ake da su a yanzu yana zama babban cikas wajen aiwatar da albashi na N70,000."
"Misali, mu ɗauki ƙaramar hukumar birnin Maiduguri (MMC), wata-wata tana karɓar kaso daga gwamnatin tarayya da ba ya wuce N700 miliyan."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Zamfara, an samu asarar rayuka

"Duk da cewa hakan na iya zama babban kuɗi a ido, wannan karamar hukuma na bukatar N778 miliyan domin biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatanta."
"Wannan na nufin dukkan kuɗin shigar wata-wata za su kare ne a biyan albashi kawai. Idan aka duba cewa akwai wasu muhimman ayyuka kamar kiwon lafiya, samar da ruwa, tsaro da sauransu da ke buƙatar kuɗi."

- Modu Alhaji Mustapha

Gwamna Zulum ya ba shugabannin kananan hukumomi aiki
Gwamna Zulum na son a samu mafita kan matsalar albashi Hoto: @ProfZulum
Source: Facebook

Gwamna Zulum na son a samo mafita

Gwamna Babagana Umara Zulum, a yayin da yake jawabi ga shugabannin ƙananan hukumomi 27, ya umarce su da su koma yankunansu domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samo mafita mai ɗorewa kan matsalar biyan albashin

“Dukkan shugabannin ƙananan hukumomi su koma yankunansu, su tattauna da masu ruwa da tsaki kuma su fito da mafita da za ta iya aiki domin warware matsalar albashi a matakin ƙananan hukumomi."
"Ina son in jaddada cewa an riga an aiwatar da biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N72,000 ga dukkan ma’aikatan gwamnati na jiha da malamai a makarantun firamare a Borno."

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an tafka barna

Wani mazaunin jihar Borno, Aliyu Bukar ya shaidawa Legit Hausa cewa dalilin da gwamnatin ta ba da ba abin yarda ba ne.

"Kawai ba su son biya ne. Idan ma'aikatan sun yi yawa su rage mana su riƙa biyan waɗanda za su iya."
"An tsaya an bar mutane kawai cikin wahala. Har yanzu akwai ma'aikacin da ke karɓar N7,000 a matsayin albashi."

- Aliyu Bukar

Malaman makaran za su shiga yajin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman makaranta (NUT) reshen jihar Kaduna ta yi barazanar tsunduma yajin aiki.

Ƙungiyar malaman ta bayyana cewa za ta shiga yajin aikin ne kan kasa biyansu mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Ta bayyana cewa an kwashe tsawon watanni ba a sanya malaman makaranta a cikin sabon tsarin biyan albashin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng