2027: Sarkin Daura Ya Fadi Wanda Masarautar Za Ta Zaba a Gaban Matar Tinubu
- Sarkin Daura ya karɓi baƙuncin uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu yayin ta'aziyyar marigayi Muhammadu Buhari
- Alhaji Umar Farouk Umar ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ne zaɓin masarautar a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara
- Mai martaba Sarkin ya bayyana cewa masarautar za ta ci gaba da marawa gwamnatin mai girma Bola Tinubu baya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar, ya yi magana kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Alhaji Umar Farouk Umar ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu shi ne ɗan takarar da masarautar Daura ke marawa baya domin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uwargidan Tinubu ta je ta'aziyyar Buhari
Uwargidan shugaban ƙasan ta jagoranci wata tawaga ta manyan mata wajen kai ziyara ta jaje ga iyalan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a garin Daura, jihar Katsina.
Sanata Oluremi Tinubu tana tare da matan shugabannin majalisar tarayya, gwamnonin jihohi, ministoci, manyan hafsoshin tsaro da sauran fitattun mata.
A lokacin da suka kai ziyara ga Hajiya Aisha Buhari, matar marigayi shugaban ƙasa, tawagar ta yi addu’o’i domin Allah ya jikan marigayin, tare da ba iyalan da ya bari haƙurin rashi.
Sanata Tinubu da tawagarta sun ziyarci kabarin da aka binne tsohon shugaban ƙasa, inda aka gudanar da addu’o'i, kafin daga bisani su wuce gidan Alhaji Mamman Daura, ɗan uwan marigayi Shugaba Buhari kuma amintaccensa.
Uwargidan shugaban ƙasan ta bayyana marigayi Buhari a matsayin ɗan ƙasa nagari wanda ya ƙawata sunan iyalinsa, garinsa, jiharsa da kuma ƙasarsa.
A nasa martanin, Alhaji Mamman Daura ya nuna godiya bisa ziyarar uwargidan shugaban ƙasa, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar girmamawa da ɗorewar zumunci.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu zai halarci taron addu'a da Allah Ya karɓi rayuwar Mai Martaba Sarki
Me Sarkin Daura ya ce kan 2027?
A fadarsa, Sarkin Daura ya karɓi gaisuwar jaje daga Oluremi Tinubu yana mai bayyana jimami da rashin ɗaya daga cikin fitattun ƴaƴan masarautar Daura.

Source: Facebook
A yayin nuna goyon baya, Sarkin ya yabawa jagorancin Shugaba Tinubu, tare da tabbatarwa Sanata Tinubu cewa masarautar Daura tana nan daram wajen marawa gwamnatinsa baya a 2027.
“Shugaba Tinubu shi ne zaɓinmu a 2027. Muna nan daram a bayansa, kuma za mu ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa domin ta samu nasara."
- Alhaji Umar Farouk Umar
ADC ta caccaki Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar haɗaka watau ADC ta caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan naɗe-naɗen muƙaman da ya yi.
ADC ta bayyana cewa Tinubu ya ba da muƙaman ne domin samun yardar mutanen Arewa waɗanda gwamnatinsa ta yi watsi da su.
Ta nuna cewa mutanen yankin ba za su bari a yaudare su ba domin sun san cewa an yi naɗe-naɗen ne ba da zuciya ɗaya ba.
Asali: Legit.ng
