Buhari: Majalisar Dinkin Duniya Ta Tura Sako na Musamman ga Tinubu, Yan Najeriya
- Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya jajanta wa Najeriya kan rasuwar Muhammadu Buhari, yana yabawa da rawar da ya taka
- Guterres ya ce Buhari ya tsaya tsayin daka wajen samar da zaman lafiya a Afirka, kuma ya goyi bayan cigaban duniya da Majalisar Dinkin Duniya
- Jakadan Najeriya ya ce ziyarar Guterres ta nuna irin darajar Buhari a duniya, musamman matsayin da ya ke da shi a Afirka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Guterres ya kai ziyarar ta'aziyya zuwa fadar Najeriya da ke birnin New York a Juma’ar da ta gabata.

Source: Twitter
Majalijar Dinkin Duniya ta jajantawa iyalan Buhari
A yayin ziyarar, Guterres ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai kishin Najeriya, Afirka da hadin kan duniya baki ɗaya, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Bidiyon Pantami ya ziyarci matar da ta reni Buhari yana jariri, ta ba shi babbar kyauta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Buhari ya bar tarihi mai ɗorewa na jagoranci da sadaukarwa, musamman wajen tallafawa zaman lafiya da gina cibiyoyi a Najeriya.
Guterres ya sa hannu a kundin ta’aziyya, inda ya nuna alhini a madadin Majalisar Dinkin Duniya da ma duniya gaba ɗaya.
Ya bayyana cewa Buhari ya kasance gwarzon jagora wanda ya jajirce wajen goyon bayan ci gaban duniya da inganta shugabanci nagari.
A cewarsa:
“Buhari zai ci gaba da kasancewa abin tunawa saboda jajircewarsa wajen hidima da kishin kasarsa da ma yankin Afirka.”

Source: Facebook
Guterres ya yabawa halayen Buhari
Guterres ya kara da cewa Buhari ya kasance mai ƙarfafa tsarin dimokiradiyya da kyakkyawan jagoranci wanda duniya ke darajawa sosai.
Ya ce ya yi aiki da Buhari kuma ya gamsu da yadda ya tsaya wajen kare martabar Najeriya da Afirka baki ɗaya.
Ya ce Buhari na da matsayi na musamman wajen tabbatar da zaman lafiya a Yammacin Afirka da goyon bayan ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa.
Ya ƙara da cewa an yaba da rawar da Buhari ya taka a ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da ci gaban yankin Yammacin Afirka.
Buhari: Guterres ya yi ta'aziyya ga yan Najeriya
Guterres ya yi wa iyalan Buhari, gwamnati da al’ummar Najeriya ta’aziyya, yana mai cewa Buhari zai ci gaba da zama abin koyi.
Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Mr. Syndoph Endoni, ya gode wa Guterres bisa ziyarar da ya kai domin ta’aziyya, The Nation ta ruwaito.
Endoni ya ce hakan ya kara tabbatar da yadda duniya ke ganin Buhari a matsayin jagora mai daraja a ƙasarsa da wajenta.
Yusuf Buhari ya yiwa Tinubu godiya
Kun ji cewa Ɗan tsohon shugaban kasa ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa mutunta mahaifinsa, Muhammadu Buhari da jana’iza ta kasa da aka shirya.
Yusuf Buhari ya yaba da goyon bayan gwamnati, Majalisa, gwamnoni da 'yan Najeriya da suka jajanta musu tare da halartar jana’izar da aka yi a Daura.
Ya fadi hakan yayin taron majalisar zartarwa na musamman da aka shirya saboda marigayin a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng
