Buhari: Tsofaffin Shugabannin Najeriya da Suka Rasu bayan Barin Mulki
- Wasu daga cikin shugabannin da suka taɓa riƙe madafun iko a Najeriya sun rasu bayan sun sauka daga mulki
- Waɗannnan tsofaffin shugabannin dai mutuwa ta riske su ne bayan sun bar fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock
- Na baya-bayan daga ciki shi ne Muhammadu Buhari wanda ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu daga cikin tsofaffin shugabannin Najeriya sun rasu bayan barin madafun iko.
Aƙalla tsofaffin shugabannin Najeriya huɗu ne suka rasu bayan barin madafun iko mafi girma a ƙasar.

Source: Twitter
Sun haɗa da shugaban ƙasa na farko na Najeriya, Dr. Nnamdi Azikiwe, shugaban Najeriya na jamhuriyya ta biyu, Alhaji Shehu Shagari, shugaban rikon ƙwarya na gwamnatin ƙasa, Cif Ernest Shonekan da Muhammadu Buhari.
Waɗannan shugabanni sun rayu bayan kammala mulkinsu, inda daga baya ajali ya riske su.
A gefe guda, akwai wasu shugabannin Najeriya da suka rasu yayin da suke kan mulki.
Abin farin ciki, har yanzu wasu tsofaffin shugabannin ƙasa, na farar hula da na soja, suna raye, ciki har da wanda ke kan mulki yanzu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
1. Nnamdi Azikiwe
An haifi Dr. Nnamdi Azikiwe a ranar 16 ga Nuwamba, 1904. Ana kiransa da “Zik na Afirka” kuma ɗaya ne daga cikin manyan shugabannin ƙasa da suka taka rawar gani wajen samun ƴancin Najeriya.
Ya zama shugaban ƙasa na farko daga 1963 zuwa 1966, bayan ya zama Gwamna Janar a 1960 tare da Firaminista Tafawa Balewa.
Azikiwe ya rasu yana da shekara 91 a ranar 11 ga Mayu, 1996, a asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke Enugu, bayan doguwar rashin lafiya.
2. Shehu Shagari
Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, shugaban ƙasan da aka zaɓa a jamhuriya ta biyu, ya rasu a ranar 28 ga Disamba, 2018, a babban asibitin ƙasa da ke Abuja, yana da shekara 93.

Kara karanta wannan
Buhari, Sheikh Abubakar Gumi da wasu jagororin Najeriya 5 da suka rasu a birnin Landan
Ya shugabanci Najeriya daga 1979 zuwa 1983 ƙarƙashin jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN), kafin a hambarar da gwamnatinsa a juyin mulkin soja a ranar 31 ga Disamba, 1983, wanda Janar Muhammadu Buhari ya jagoranta.
3. Ernest Shonekan
Cif Ernest Shonekan ya rasu a ranar 11 ga Janairu, 2022, yana da shekara 85, sakamakon ciwon huhu a wani asibiti da ke Legas.
Ana tunawa da shi ne saboda rawar da ya taka a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na gwamnatin ƙasa a 1993 a mulkin wucin gadi wanda ya ɗauki ƴan watanni kaɗan kafin Janar Sani Abacha ya karbe mulki.
Jaridar Daily Trust ta ce iyalansa sun tabbatar da cewa ya yi mutuwa ce ta Allah da Annabi.
4. Muhammadu Buhari
Janar Muhammadu Buhari ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a birnin Landan yana da shekara 82.

Source: Twitter
Tsohon mai magana da yawun bakinsa, Garba Shehu, ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa na X.
An haife shi a ranar 17 ga watan Disamba, 1942, a Daura, jihar Katsina.
Ya zama gwamnan soja na tsohuwar Borno da Arewa ta Tsakiya daga 1975 zuwa 1976, inda ya fara nuna kwarewa a harkokin shugabanci.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya sa labule da gwamnan da ya sauya sheƙa zuwa APC, an samu bayani
Buhari ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2015 ƙarƙashin jam’iyyar APC. An sake zaɓensa a 2019.
Kwankwaso ya je ta'aziyyar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya je jihar Katsina.
Kwankwaso ya je Katsina ne domin ta'aziyyar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.
Tsohon shugaban ƙasan dai ya rasu ne bayan ya yi jinyar rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin Landan.
Asali: Legit.ng
