An binne marigayi tsohon shugaban kasa Shagari a mahaifar sa, hotuna
A yau, Asabar, ne aka binne gawar tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a mulkin dimokradiyya, Marigayi Alhaji Shehu Shagari, a mahaifar sa, karamar hukumar Shagari, dake jihar Sokoto.
Tsohon shugaban jami'ar Usman Danfodio Sokoto, Farfesa Shehu Galadanchi, ne ya jagoranci sallar jana'izar tsohon shugaban kasar da misalin karfe 3:30 na rana.
Tun da farko, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, tare da manyan jami'an gwamnatinsa sun tarbi gawar tsohon shugaban kasar a filin tashi da saukar jiragen sama na Sultan Abubakar dake garin Sokoto.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci jana'izar marigayi Shagari akwai sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, gwamnonin jihohin Kebbi da Zamfara.
DUBA WANNAN: Aliyu Aminu: An kara gano wani matashin soja da ya mutu a sabon harin Boko Haram, hotuna
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, tsohon minsta, Mukhtar Shagari, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, da sauransu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng