Yadda Shugaba Tinubu Ya 'Kunyata' Gwamna Abba a Ziyarar da Ya Kai Jihar Kano
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bai samu zuwa gidan gwamnatin Kano ba yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai gidan Aminu Ɗantata
- Rahotanni daga fadar gwamnatin sun nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna ɓacin ransa kan lamarin saboda an shirya liyafar cin abinci
- Haka nan kuma Tinubu ya ƙauracewa kai gaisuwa wurin sarakunan Kano biyu, Sanusi II da Aminu Ado don gudun nuna ɓangaranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya koma gida cikin ɓacin rai bayan ziyarar da Shugaba Bola Tinubu ya kai jihar ranar Juma'a, 18 ga watan Yuli.
Gwamnan bai ji daɗi ba sakamakon rashin zuwan Shugaba Tinubu fadar gwamnatin Kano ballantana ya ci abincin da aka tanadar masa.

Source: Facebook
Tinubu ya kauracewa fadar Sanusi II da Aminu
Haka kuma, shugaban ƙasa bai kai gaisuwa ga kowanne daga cikin mutanen biyu da ke rikici kan kujerar Sarkin Kano ba, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, in ji Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya je Kano ne a ranar Juma’a domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a ranar 28 ga Yuni, 2025 a Abu Dhabi.
A mafi yawan lokuta, shugaba ƙasa kan ziyarci gidan gwamnati da fadar Sarki idan ya kai ziyara wata jiha a Arewacin Najeriya, amma a wannan karon iyakar Tinubu gidan marigayi Dantata.
Gwamna Abba ya nuna ɓacin ransa
Majiyoyi daga gidan gwamnati sun bayyana cewa Abba, wanda kafin ziyarar ya buƙaci Kanawa su tarbi Tinubu da mutunci da girmamawa, ya fusata bayan fadar shugaban ƙasa ta sanar da tsarin ziyarar.
Gwamna Abba da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin sun tarbi Shugaba Tinubuɓa filin jirgin sama na Aminu Kano.
A wurin magoya bayan jam’iyyar APC sanye da riguna da hoton Shugaba Tinubu sun riƙa rera waka mai taken “Omo Ologo”.
A cewar majiyoyi daga fadar gwamnatin Kano, Gwamna Abba ya gano cewa shugaban ƙasa ba zai je gidan gwamnati ba ne a lokacin da ya isa gidan marigayi Dantata.
An ce tun a wurin Abba Kabir ya bayyana ɓacin ransa matuƙa ga masu kula da tsarin tafiyar shugaban ƙasa.

Source: Facebook
Me yasa Tinubu ya kauracewa fadar sarakuna 2?
Majiyar ta ce abincin da aka tanada don Shugaba Tinubu daga bisani ma’aikata da masu gyaran lambun gidan gwamnati suka ci, bayan sun tabbatar Tinubu ya koma Abuja.
A bangare guda, Shugaba Tinubu ya kauce wa haɗuwa sarakunan biyu, Sanusi II da Aminu Ado domin kada a zarge shi da nuna bangare a rikicin sarautar Kano.
Rikicin sarautar ya fara ne a watan Mayu 2024 bayan Gwamna Yusuf ya tube Aminu Ado Bayero da wasu sarakunan gargajiya guda huɗu, sannan ya dawo da Muhammadu Sanusi II.
Me ya hana Ganduje zuwa tarbar Tinubu?
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai je wurin tatbar Shugaba Tinubu a Kano ba saboda yana Landan.
Tsohon hadimin Ganduje, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan yayin da aka fara surutu kan rashin ganin tsohon gwamnan a wurin tarbar shugaban ƙasa.
Garba ya jaddada cewa Ganduje yana da kyakkyawar alaƙa da Tinubu, kuma murabus dinsa bai shafi haɗin kansu da jam’iyyar APC ba.
Asali: Legit.ng

