Hotunan Sanusi II Ya Buɗe Sabon Masallaci a Kano, Ya Jagoranci Limanci na Farko

Hotunan Sanusi II Ya Buɗe Sabon Masallaci a Kano, Ya Jagoranci Limanci na Farko

  • Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jagoranci bude sabon masallacin Jumu’a a Zawaciki, Kano, inda ya gabatar da huduba da salla ta farko
  • Masarautar Kano ta bayyana cewa masallacin da aka bude a ranar 18 ga Yuli 2025, ana kiransa Alansar Wal Muhajirun
  • An bayyana Sarki Sanusi II a matsayin magaji ga tsarin Shehu Usman Ɗan Fodio, yayin da ya jagoranci limanci a sabon masallacin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya jagoranci limanci a wani sabon masallacin da ya bude wanda aka gudanar a jiya Juma'a a birnin Kano.

Sarkin ya kaddamar da sabon masallacin Juma'a a jihar a jiya 18 ga watan Yulin 2025 a birnin Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sanusi II ya buɗe sabon masallacin Juma'a
Sarki Sanusi II ya yi limanci a sabon masallacin Juma'a a Kano. Hoto: @AbdallahVox.
Source: Twitter

Shafin Masarautar Kano ne ya yada hotunan Sarkin yayin buɗe masallacin a jiya Juma'a wanda @AbdallahVox ya wallafa manhajar X.

Kara karanta wannan

"Ina kewarsa," Tinubu ya faɗi alaƙarsa da Ɗantata yayin ta'aziyya a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II ya jagoranci sallar jana'iza a Kano

Wannan bikin bude masallacin ya biyo bayan babban rashi da masarautar Kano ta yi na wasu daga cikin iyalan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi I a fadar.

Sarki Sanusi II shi ya jagoranci sallar jana'izar mamatan guda biyu a Kano a ranar Laraba 16 ga watan Yulin 2025 da muke ciki.

Masarautar ta shiga jimami bayan rasuwar iyalin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Yaya Jide da 'yarsa, Goggo Ummahani a makon da ya gabata.

Sanusi II ya iske rashi bayan dawowa Najeriya

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya jagoranci sallar jana’izar a ranar Laraba ne bayan ya dawo daga kasar Birtaniya.

Marigayi Sarki Sanusi I ya mulki Kano daga 1954 zuwa 1963, kuma Sanusi II ya fara hawan karagar 2014, sannan ya sake komawa a 2024.

Sarki ya bude sabon masallacin Juma'a a Kano
Sarki Sanusi II ya jagoranci sallar Juma'a a sabon masallaci da ya kaddamar. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

Sanusi II ya bude sabon masallacin Juma'a

Kara karanta wannan

Abin da Sarki Sanusi II ya yi a fadarsa domin karrama marigayi Buhari

Sarki Sanusi II ya ci gaba da yiwa addinin Musulunci hidima bayan budewa, gudanar da huduba da kuma jagoranta sallar Juma'a ta farko a masallacin.

Sanarwar ta ce Sarki Sanusi II ya kaddamar tare da bude sabon masallacin Alansar Wal Muhajirun a Zawaciki.

Bayan bude masallacin, Sarki Sanusi II ya yi huduba mai kama hankali da kuma jagorantar limancin farko a masallacin.

Sanarwar ta ce:

"Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II PhD CON, Sarkin Kano, ya kaddamar da sabon masallacin Jumu’a na Alansar Wal Muhajirun da aka gina a Zawaciki, Jihar Kano.
"Ya kuma ya gabatar da huduba da sallar Jumu’a ta farko a masallacin.
"Magaji kenan ga tsarin Shehu Usman Ɗan Fodio."

Buhari: Sanusi II ya umarci saukar da tuta

A baya, mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Tun farko, fadar Sanusi II ta nuna alhini kan rasuwar bayan tura sakon ta'aziyya tun ranar mutuwar Buhari wanda ya rasu a birnin London.

A cikin wani bidiyo, an gano yadda aka yi kasa-kasa da tuta da ke saman fadar domin nuna jimami saboda rasuwar Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.