Rasuwar Buhari: An Fara Cacar Baki tsakanin Mutanen Tinubu da Atiku
- Fadar shugaban kasa ta bayyana zargin ADC a kan jana’izar shugaba Muhammadu Buhari a matsayin abin dariya
- Mai magana da yawun shugaban kasa ya ce ADC na kokarin neman suna ne da amfani da rasuwar Buhari
- Gwamnatin Bola Tinubu ta ce ta gudanar da jana’izar Buhari da girmamawa kamar yadda ya dace da darajarsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare, ya mayar da martani mai zafi a kan jam’iyyar ADC, yana mai cewa tana amfani da rasuwar shugaba Muhammadu Buhari don neman farin jini.
A cewar Dare, wannan zargi da ADC ta yi wa gwamnatin Bola Tinubu cewa tana amfani da rasuwar Buhari don siyasa ba gaskiya ba ne.

Source: Twitter
Legit ta gano cewa fadar shugaban ta yi wa jam'iyyar ADC martani a wani sako da ta wallafa a X a yau Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta wallafa cewa ya ce zargin ADC wani yunkuri ne na neman suna da jam'iyyar ke yi saboda tana fama da matsaloli.
Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ADC ke fitar da irin wannan sanarwa mai cike da rashin hangen nesa da neman daukar hankali ba.
Zargin da ADC ta yi wa Tinubu kan Buhari
Jam’iyyar ADC ta fitar da wata sanarwa da ke zargin gwamnatin shugaba Bola Tinubu da siyasantar da rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Vanguard ta wallafa cewa ADC ta ce gwamnatin ba ta nuna girmamawa yadda ya kamata ba wajen jana’izar Buhari.
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da zargin, inda Sunday Dare ya bayyana jam’iyyar a matsayin maras tushe da ke kokarin amfani da rasuwar don neman gindin zama a siyasar Najeriya.
Ya ce:
"ADC ta fi kowa yin amfani da rasuwar Buhari don jawo hankali da neman suna."
Sunday Dare ya kare gwamnatin Tinubu
Dare ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba ta bukatar neman suna ta hanyar siyasantar da mutuwa, domin nasarorin da take samu na tabbatar kokarinta.
Ya ce gwamnatin ta gudanar da jana’izar Buhari da cikakken girmamawa da janyo halartar shugabannin kasashe da dama.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin na samun ci gaba a fannoni da dama:
“Ana fitar da danyen mai fiye da ganga miliyan 1.7 a rana, kuma kudin da ake rabawa jihohi ya karu da 60%. Jihohi 31 da ke cikin bashi yanzu suna iya biyan albashi da fansho.”
'ADC na siyasantar da rasuwar Buhari,' Dare
Sunday Dare ya ci gaba da cewa ADC ta riga ta lalace a siyasa, kuma kokarin da take yi yanzu na zuwa kabarin Buhari don neman goyon bayan jama’a ba.
Ya kuma soki irin yadda wasu ‘yan siyasa suka yi amfani da halartar jana’izar Buhari a Daura don cin gajiyar siyasa, yana mai cewa gwamnatin Tinubu ta fi karfin wasa da mutuwa.
An radawa Buhari takwara a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa wani bawan Allah a jihar Bauchi mai suna Danladi Mai Kaset ya yi wa Muhammadu Buhari mai suna.
Danladi Mai Kaset ya sanya wa Buhari mai suna ne domin gwagwarmayar da tsohon shugaban kasar ya yi a baya.
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya ba mutumin kyautar kudi har N200,000 domin sayen ragon suna.
Asali: Legit.ng


